Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba sun bayyana cewa mutum 8 suka rasa rayukansu a rikici tsakanin kabilun Kutep da Fulani a kauyukan Kwe Sati da Fikye, karamar hukumar Ussa.
Kakakin rundunar Abdullahi Usman da ya sanar da haka ya ce akwai yiwuwar za a samu mutane da yawa da suka ji rauni a sanadiyyar wannan rikici.
Usman ya tabbatar cewa rundunar za ta gudanar da bincike kan rikicin yana mai cewa rikicin kabilar Kutep da Fulani rikici ne da suka dade suna yi a jihar.
“A rikicin Ketup da Fulani da aka yi a makon jiya ya yi sanadiyyar rayukan mutane 8 sannan akwai Wani rikicin da aka Yi da ba zan iya tabbatar da yawan mutanen da suka mutu ko suka ji rauni ba domin haryanzu a na bincike a kai.
Usman ya ce zuwa yanzu zaman lafiya ya fara dawowa a karamar hukumar.
Bayan haka Shugaban karamar hukumar Ussa Abershi Musa ya sauka daga kujeransa na Shugaban karamar hukumar. Dalilin sa na sauka daga shugabancin karamar hukumar kuwa shine zargin da yake yi cewa wai gwamnati bata damu da yadda fulani ke kashe ƴan kabilar Kutep ba.
Discussion about this post