Ɗan takarar gwamnan Kaduna na jam’iyyar APC, sanata Uba Sani ya lashe zaɓen gwamnan jihar .
Hakan na ƙunshe ne a sanarwar da Baturen zaɓen gwamnan johar ya sanar a garin Kaduna ranar Litinin a Kaduna.
Farfesa Lawal Suleiman Bilbis, Shugaban Jami’ar Usman Ɗanfodio da ke Sokoto ya shaida cewa Sanata Uba Sani ya samu Kuri’u 730,002 inda shi kuma Isah Ashiru na PDP ya samu Kuri’u 719,196.
Ɗan takarar jam’iyyar Labour Jonathan Asake ya zo na uku da kuri’u 58,283 sai kuma sanata Suleiman Hunkuyi na NNPP da ya samu Kuri’u 21,405.
Discussion about this post