an takarar gwamnan jihar Kaduna na Jam’iyyar PDP, Isah Ashiru ya mika sakon godiyar sa ga mutanen jihar Kaduna bisa goyon bayan da suka nuna wa jam’iyyar a zaɓukan ƴan majalisun tarayya da na majalisar dattawa.
A hira da yayi da manema labarai, ranar 1 ga Maris, Isah ya roki mutanen Kaduna su fito su kare sa aikin da suka fara na fidda kansu daga ƙangi da matson da ka saka su.
” Ku fito ku karisa abinda kuka fara ranar 11 ga Maris. Idan kuka yi haka riba biyu za ku samu, na farko ribar fidda kai da ɗan uwanka daga kangi da wahala, wanda idan mutum yayi zai samu lada sai kuma ribar da za a samu na kwankwaɗar romon dimokuraɗiyya da za ku samu daga gwamnatin da zamu kafa.
Idan ba a manta ba, jam’iyyar PDP ta yi nasarar gaske a zaɓukan da aka kammala a makon jiya a jaihar Kaduna inda ta lallasa APC mai Mulki a kananan hukumomin jihar.
Ranar 11 ga Maris ne za agudanar da zaɓukan gwamna da na majalisun jihohi.
Malam Uba Sani ne zai kara da Isah Ashiru na PDP a zaɓen da kuma sauran ƴan takara da ke wasu jam’iyyun.