Ƙungiyar Kishin Ƙabilar Yarabawa Zalla, wato Afenifere ta bayyana kakkausan furucin da Shugaban Majalisar Dattawan Ƙabilar Igbo, Emmanuel Iwuanyanwu ya yi kan Yarabawa da cewa kalamai ne masu rura wutar raba kan jama’a da cusa ƙiyayya tsakanin ƙabilun biyu.
Iwuanyanwu wanda shugaban dattawan Ohaneaze Ndigbo ne, ya kira waɗanda su ka nuna wa ƙabilar Igbo tsana da tsangwama lokacin zaɓen 2023 a Legas cewa “yan iskan ‘yan siyasa ne.”
Iwuanyanwu ya yi furucin ranar Lahadi a Awka, babban birnin Jihar Anambra.
Ya yi furucin a lokacin da ya ke jawabi wurin taron murnar cikar Gwamnatin Charles Soludo shekara ɗaya kan mulki.
Ya yi maganar ne matsayin raddin jin ra’ayin sa kan taho-mu-gamar da aka riƙa gwamzawa tsakanin Yarabawa da Igbo a Legas, a ranar zaɓen gwamna a Legas.
Iwuanyanwu ya yi tir da rikicin kuma ya gargaɗi Yarabawa kada su sake tsokanar ƙabilar Igbo da rigima.
Sai dai kuma a ranar Lahadi, Ƙungiyar Afenifere ta maida masa raddi ta hannun Sakataren Shirye-shirye na ƙungiyar, Kole Omololu.
Omololu ya ragargaji Iwuanyanwu, sannan kuma ya ja kunnen ‘yan Najeriya, musamman Yarabawa cewa su nisanci tashin hankali, su rungumi zaman lafiya da kyakkyawar zamantakewar mu’amala da sauran ƙabilu.
Sai dai kuma a ranar Lahadi, Iwuanyanwu ya musanta cewa ya kira Yarabawa ‘yan iskan ‘yan siyasa. Ya ce wanda duk ya yaɗa wannan ƙarya, to ƙazafi ne ya yi masa, bai faɗa ba.
Ya ce, a wurin taron Gwamnan Anambra ne ya nuna farin cikin ganin yadda jama’a daga ko’ina har daga Legas da Turai, Canada da Amurka sun je Awka.
Shi ne na ce masu waɗanda su ka je daga Legas idan sun koma Legas su shaida wa sauran ‘yan uwan mu da ke can cewa daga yau ba zamu sake barin aka kashe su a banza a wofi bar. Duk wanda ya taɓa ku, za mu taɓa shi.
“Mu na ko’ina a Najeriya, kuma mun zuba jari da kadarori ko’ina a Najeriya. Duk wanda ya ce mu fice daga garin su, ba za mu fita ba.
“Kuma ina so na sanar da ku cewa babu wani yaƙi tsakanin mu da Yarabawa, domin su Yarabawa ai ‘yan iskan ‘yan siyasa ne, za mu iya bi da su.”
Afenifere ta gargaɗi Dattawan Ndigbo cewa su ja kunnen Inwuanyawu kada ya ƙara cin mutuncin ƙabilar Yarabawa.
Discussion about this post