Kwamishinan lafiya na jihar Filato Nimkong Ndam ya koka da yadda tarin fuka ke ci gaba da yaduwa a jihar.
Kwamishinan ya koka da haka a taron ranar cutar na duniya da aka yi a kauyen Gyel dake karamar hukumar Jos ta Kudu ranar Juma’a.
Ya ce zuwa yanzu sakamakon bincike ya nuna cewa mutum 229 daga cikin mutum 100,000 sun kamu da cutar a jihar.
Binciken ya nuna cewa a shekarar 2021 mutum 10,000 na dauke da cutar a jihar.
“Burin wannan taron shine wayar da kan mutane game da cutar.
“Zuwa yanzu muna bai wa mutanen dake cikin hadarin kamuwa da cutar magani domin kare su daga kamuwa da cutar.
“Yin haka zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar saboda mutum daya dake dauke da cutar zai iya yadawa mutum 15 lokaci guda.
“A taron burin mu shine mu gano masu fama da cutar domin basu magani.
Shugaban kungiya mai zaman kanta na jihar Filato ‘ Breakthrough Action Nigeria’ Catherine Igoh ta ce burin shirya taron shine wayar da kan mutane game da cutar domin dakile yaduwar ta.
Ta Yi kira ga mutane da su rika gaggawar zuwa asibiti da sun fara fama da tarin da baya Jin magani.
“Maganin tarin fuka kyauta ne inda hakan ya sa muke kira ga mutane da su garzaya asibiti domin yin gwajin cutar da karbar magani.
Bayan haka Shugaban kwararrun likitocin Najeriya reshen jihar Filato Chudung Miner ta ce rashin zubar da shara da tsaftace muhalli na daga cikin matsalolin dake yada cutar.
Discussion about this post