Kamfanin Fetur na Najeriya, NNPC, ya bayyana cewa matsalar ƙarancin fetur da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, ba maƙarƙashiyar gurgunta zaɓen 2023 ba ce.
Shugaban Kamfanin NNPC, Mele Kyari ne ya bayyana haka yayin da ake tattaunawa da shi a gidan talabijin na NTA, a Abuja, ranar Alhamis.
Cikin makon da ya gabata ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya yi kakkausan furuci a ziyarar kamfen ɗin da ya kai Jihar Ogun, inda ya ce an ƙirƙiro matsalar fetur da sauya launin kuɗi don a kayar da shi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Amma da ya ke magana a ranar Alhamis, Kyari ya ce wasu a
al’amurra ne na masu wuyar lamari su ka kawo kiki-kaka a tsarin rarraba fetur, shi ya sa ake fama da ƙarancin sa a faɗin ƙasar nan.
“A yau ɗin nan da na ke magana da ku, akwai motocin tanka-tanka na tirela 38,000 da ke kan hanyar zuwa jihohi daban-daban.” Inji Mele Kyari.
“Inda kawai matsalar ta ke shi ne, ko yaya aka ce an ɗan samu wani tsaiko kaɗan, to sai wasu su yi amfani da matsalar har ta kai ga samun wasu ɓatagari su kawo harkar bunburutu a lamarin.
“Amma ba gaskiya ba ne ga masu cewa wai an ƙirƙiro matsalar ƙarancin fetur don a kawo wa zaɓen 2023 cikas. Wannan ƙarancin fetur da tun cikin 2022 aka soma ta.
“Bari ku ji. A ƙasar nan idan aka samu matsalar rarraba fetur ta tsawon kwanaki uku, sai a yi makonni uku kafin a shawo kan ta.”
Discussion about this post