Kotun majistare dake Ikeja jihar Legas ta gurfanar da wata Uwar adashi mai suna Owolabi Falilat ranar Tatata bisa laifin cinye wa mutane kudaden adashe har naira 850,000.
Kotu ta tsare Falilat bisa laifin zamba cikin aminci.
Sai dai kuma duk da hujjojinnda ake dasu na tabbacin ta laƙume kuɗin, Falilat ta musanta laifin da ake zargin ta da shi a kotu.
Dan sandan da ya shigar da kara sifeto Mathew Amos ya bayyana a kotun cewa rundunar ta kama Falilat ranar 13 ga Janairu bayan dadewa da aka yi ana nemanta ruwa a jallo.
Ya ce daga watan Yulin 2021 zuwa Afrilun 2022 Samuel Florence, Aluko Falilat da Aminat Ogunmokun sun tara Naira 850,000 a ha nun Falilat kudin adashi inda Falilat ta yi sama da fadi da su.
Amos ya ce daga watan Yuli zuwa Disamba Falilat ta yi wa masu adashen ta barazanar cewa za ta yi maganin duk masu aiko mata da sakonnin barazana ta tes ko ta murya a whatsapp da kira ta wayar salula.
Lauyan dake kare Falilat, Akintan Olukayode ya ce Falilat da ƴan adashen na kokarin sasanta kansu a wajen kotu.
“A yanzu haka Falilat da masu adashen ta sun yake shawaran lokaci da yadda Falilat za ta biya kowa kudinsa.
Alkalin kotun Mrs I. O Raji wacce ba ta ji dadin abincda ya faru ba ta tambayi masu adashen ko sun kawo kara kotu domin tsorata Falilat ta biya su kudaden su ne
Raji ta gargaddin mutane da kada su yi wasa da kotu domin kotu ba wurin wasa bane sannan ta umurci lauyan dake kare Falilat, Olukayode da ya nemi belin Falilat.
Alkali ta Bada belin Falilat akan Naira 150 tare da gabatar da shaidu biyu sannan ta tabbatar cewa daya daga cikin shaidun da zata gabatar dan uwan ta ne na jini.
Za a ci gaba da shari’a ranar 21 ga Janairu.
Discussion about this post