Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bukaci hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta cafke dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar bisa zargin cin hanci da rashawa.
Kamfen din ya kuma bayar da wa’adin sa’o’i 72 ga hukumar EFCC, da hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC), da kuma hukumar da’ar ma’aikata (CCB), da su kamo jagoran ‘yan adawar.
Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Festus Keyamo, a wata kara mai dauke da kwanan watan 16 ga watan Janairu, ya bukaci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da su kamo tsohon mataimakin shugaban kasar bisa laifukan da suka shafi halasta kudaden haram, karya dokar da’a, hada baki, da kuma aikata laifukan cin amana da almubazzaranci.
A cewar Keyamo, Kwamitin yakin neman zaben Tinubu na aiki ne a kan zargin da Michael Achimugu ya yi, wanda ya yi ikirarin cewa shi tsohon mai taimaka wa dan takarar PDP ne, Atiku Abubakar.
Ministan ya ce wanda ake zargin ya bayar da “wasiku, takardu, faifan sauti, rantsuwa da kuma shaidarsa ta baka kai tsaye kan yadda Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, a lokacin da yake mataimakin shugaban Najeriya a tsakanin 1999 zuwa 2007, ya hada baki da maigidansa na wancan lokacin, Olusegun Obasanjo, domin talauta kasar nan tare da sace dukiyar jama’a ta hanyar amfani da abin da ya kira “(SPVs)”.
A wani taron manema labarai na hadin gwiwar daraktan yada labarai na yakin neman zaben APC a ranar Litinin, jam’iyyar ta bukaci Atiku ya janye daga takarar.
Keyamo ya kara da cewa dole ne Atiku ya mayarwa gwamnatin tarayya dukkan kudaden da ke cikin “SPV” sannan ya gabatar da kansa domin bincike da gurfanar da shi gaban kuliya.