A yau Laraba ne aka yi muhawara tsakanin ‘yan takarar gwamnoni na jihar Kaduna a dakin taro na Jami’ar Kaduna. A wurin wannan taro ‘yan takara sun amsa tambayoyi daga mutane da a wasu lokuttan akan kaure da cacan baki domin tabbatar da hujjojin su ga mutane.
‘Yan takarar sun amsa tambayoyi kan bunkasa Ilimi, tattalin arziki, ayyukan noma, da matasa da mata.
Uba sani ya ce ” Zamu taimaki manoma, mu maida hankali wajen taimakawa manoman mu da kayan aiki domin noma musamman amfanin gona wanda jihar Kaduna ta yi fice akan su. Kamar su Shinkafa, Acca, Citta, da sauransu.
Bayan haka sanata Uba Sani ya yabawa gwamnati mai ci cewa ta bunkasa fannin Noma ta hanyar kakkafa masana’antu da suka dauki dubban matasa aiki a jihar.
A nashi jawabin Honarabul Isah Ashiru dan takarar gwamnan jihar na PDP, ya bayyana cewa zai maida hankali ne wajen tabbatarwa da ganin kananan manoma sun koma gona.
Haka shima sanata Suleiman hunkuyi na NNPP ya ce zai bunkasa harkar gona ne ta hanyar fadada filaye a jihar da saka jari babba domin talakawa su koma gona suma.
Sai dai kuma a lokacin da ake bada amsoshi, akan kaure da cacan baki inda ‘yan takara ke kokarin kare kansu da jam’iyyar su bisa manufofin da suka saka a gaba.
Discussion about this post