Jirgin kasa da ya taso daga Abuja-Kaduna ya murkushe wata mota a unguwar Chikasoro dake cikin yankin Kubwa daka Abuja.
Rundunar ‘yan sandan Abuja ta tabbatar da afkuwar wannan hatsari a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis.
Mai magana da yawun rundunar Josephine Adeh ta hukumar jirgin sun ƙaddamar da bincike kan faruwar lamarin sannan ta ce za a mayar da alamun kan hanya da gyara wadanda ake da su don kaucewa faruwar makamancin irin wannan hadarin.
Idan ba a manta ba an shafe watanni 9 jirgin baya aiki tun bayan harin da ƴan ta’adda suka aki wa jirgin a Maris.
Discussion about this post