Bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya ƙaurace wa duk wani zaman ‘ta-tambaya-ja-jawabi’, ‘mahadara’, ‘mujadala’ ko ‘maƙabalar’ da aka gayyace shi har sau huɗu a Najeriya, sai ga shi a ranar 5 Ga Disamba ya jagoranci tawagar da ya je Chatham House na birnin Landan, inda ya yi jawabin bayyana manufofi da ƙudirorin sa idan ya kafa gwamnati a zaɓen 2023.
Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar APC Bola Tinubu, ya bayyana cewa lallai yawan hare-haren banka wa ofisoshin INEC wuta da yanzu ake yi, abin damuwa ne sosai kafin zuwan zaɓen 2023.
Tinubu ya nuna wannan damuwar a lokacin da ya ke jawabi a taron Chatham House, a Landan, ranar Litinin.
A wurin taron inda ya bajekolin manufofi da ƙudirorin gwamnatin da zai kafa idan ya yi nasara a zaɓen 2023, ya ce batun tsaro da tashe-tashen hankulan zaɓe abin damuwa ne sosai a ƙasar nan, musamman ganin yadda abin ke ƙara muni, daidai lokacin da zaɓen 2023 ke gabatowa.
Ya ce kai wa ofishin INEC hari da kuma tashe-tashen hankulan siyasa su ne manyan barazanar da ke tunkarar zaɓen 2023.
Daga nan ya yi kira ga sauran ‘yan takara su jajirce wajen ganin an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali, domin bai wa talakawa damar samar wa alƙiblar su fuskar ci gaba da wanzuwa.
Daga nan ya yi alƙawarin idan ya zama shugaban ƙasa, zai wadata Najeriya da wutar lantarki, ta hanyar yi wa fannin makamashi gagarimin garambawul.
“Harkar makamashi abu ne mai muhimmanci. Babu wani ɓangaren da zai iya bunƙasa a ƙasar nan ba tare da wadatacciyar makamashi ba.”
Batun ilmi kuwa, Tinubu cewa ya yi zai samar da lamunin da za a riƙa bai wa ɗalibai kuma zai farfaɗo da tsarin inganta karatun almajirai.
Sannan kuma ya yi alƙawarin samar da ƙarin malamai tare da bayar da horo ga malamai domin a ƙara wa ilmi inganci da nagarta.
Batun Takamaimen Shekarun Sa:
Tinubu ya ce an haife shi a ranar 29 Ga Maris, 1952. Haka shekaru na su ke har a jami’a. Masu ɓata lokacin shan wahalar bin diddigin gano shekarun sa, sun gane wahalar banza su ke yi, kuma su na ta asarar kuɗin su.”
Ya ce shi iyalan gidan Tinubu ne, kuma ya ragargaji masu yi masa yarfen cewa shi ba ɗan Najeriya ba ne.
“Ni Tinubu ne uba na. Shi ya haife ni. Wanda ke tantama kuwa, to har sakamakon DNA za a iya bai wa mai shakkun haka.” Inji shi.
“Haka nan kuma Jami’ar Jihar Chicago da ke Deloitte wacce na ji digiri, ta tabbatar da karatun da na yi a can. Ta maido min satifiket ɗi na da ya ɓata, wato ta sabunta mun sani kwafen.”
Cikin waɗanda su ka raka Tinubu, har da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila, Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna, Badaru Abubakar na Jigawa, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas, Gwamna Ben Ayade na Cross River.
Akwai irin su Kayode Fayemi, tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Shugabar Matan APC, Betta Edu, tsohon Kwamishinan Kuɗi na Jihar Legas, Wale Edun.
An yi masa tambayoyi 10, ya masa huɗu, ya raba shida ga sauran ‘yan tawagar da ya je da su, ya ce kowa ya amsa ɗaiɗai.
Ya ce hakan ya na nufin cewa zai yi gwamnati mai cike da gigaggu kuma ƙwararru.
Sai dai kuma Rundunar Yaƙin Atiku Abubakar ta ce zuwa Tinubu Chatham House abin kunya ne. Ta ce ya guje wa zuwa taron ganawa da shi a nan Najeriya inda masu zaɓe su ke, ya je Landan, a can ma ya kasa amsa wasu tambayoyi, ya miƙa wa muƙarraban sa su amsa masa.
Discussion about this post