A ranar Juma’a ce Kotun majistare dake Iyaganku a jihar Oyo ta yanke wa Opeyemi Ajala mai shekara 40 hukuncin zaman kurkuku bisa zargin yi wa ‘yar cikinsa mai shekaru 21 fyade.
Alkalin kotun Emmanuel Idowu ya yi watsi da rokon sassaucin da Ajala ya nema saboda rashin ikon yanke hukuncin akan karar.
Sannan kuma Idowu ya ce Ajala zai yi zaman kurkukun dake Abolongo a garin Oyo har sai kotun ta kammala yin shawara da fannin dake gurfanar da masu aikata laifuka irin haka na jihar.
Ya ce za a ci gaba da shari’a ranar daya ga Fabrairu 2023.
Bayan haka lauyan da ya shigar da karar Amos Adewale ya ce rundunar ‘yan sanda ta kama Ajala bisa ga laifin yi wa ‘yar sa fyade.
Adewale ya ce Ajala ya yi wa ‘yarsa fyade a watan Agusta a gidan sa dake Gaa Legbedu a Ogbomoso.
Idan har aka kama Ajala da laifin fyade za a Yi masa hukuncin daurin rai da rai tare da an yi masa bulala bisa ga dokar ‘Criminal code’ ta jihar Oyo ta shekaran 2000.
Discussion about this post