Babban Kwamandan Jiragen Shugaban Ƙasa ya nuna rashin jin daɗin yadda bashi ya yi wa jiragen katutu, saboda ƙarancin wadataccen kasafin kuɗi.
Rashin wadatattun kuɗaɗen tafiyar da gyare-gyaren da sauran ayyukan da su ka jiɓinci jiragen ya kai ga tilas wasu ayyukan gyare-gyare da sauran su, duk a bashi ake aiwatar da su.
Kwamandan Jiragen Shugaban Ƙasa, Abubakar Abdulahi ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, lokacin da Kwamitin Majalisar Wakilai ta Ƙasa mai lura da Al’amurran Tsaro da Ayyukan Sirri ya kai ziyarar gani da ido a bargar jiragen Shugaban Ƙasa ɗin a Abuja.
Abdulahi dai ya samu wakiltar Babban Jami’in Kula da Jiragen, ya ce ƙarancin kuɗaɗen da ake bai wa jiragen a sun shafi gudanar da ayyukan jiragen.
Ya tunatar da kwamitin cewa sun aika da buƙatar naira biliyan 18.767, amma aka rage kasafin a majalisa zuwa Naira biliyan 12.550.
Daga nan ya ce ko a kasafin 2021 har yanzu cikin Disamba na a cika masu naira biliyan 10.9 ba.
Ya ce a kasafin 2019 kuwa, an rattaba cewa za a kashe Naira biliyan 19,469,313,645, sai aka rage shi zuwa naira bilyan 12.475.
Ya shaida wa kwamiti cewa kuɗin ayyukan kula da jiragen na Shugaba Buhari.
“Ina tabbatar maku cewa kashi 45 bisa 100 na kuɗaɗen kasafin jiragen Shugaban Ƙasa, duk a wajen gyare-gyare da kula da jiragen.
Ya ce akasarin bashi ya yi katutu, har na shekarar da ta gabata ya na iske na bana, ko ma na shekara mai zuwa. Kuma yawancin masu bin waɗannan basussuka duk a kasashen waje su ke.
“Ya na da kyau ku sani cewa yawancin jiragen nan sun kai shekaru 11 ana tafiyar da su. To matsalar jirgin sama ita ce yayin da jiragen su ka ƙara shekaru, farashin kayan gyara da aikin sa ƙara tashi sama su ke yi.
Ya ƙara da cewa kuɗin yi wa jirgi daga kuɗin kula da gyaran jirgi ɗaya kan kama daga naira milyan 1.5 zuwa naira bilyan 4.5.
Daga nan ya ce a 2023 jiragen za su sha zirga-zirgar jiragen za ta ƙaru sosai saboda halarta kamfen zuwa jihohi daban-daban.
Shugaban Kwamitin Sha’aban Sharaɗa, ɗan ADP daga Kano, ya ce kwamitin zai yi bakin ƙoƙarin da zai yi domin ya ga an magance matsalolin.
Discussion about this post