Kafin zaɓen 2015, kusan kowa na yi wa Shugaba Muhammadu Buhari kallon wani barden yaƙi da cin hanci, rashawa, kuma saboda haka ne ma ya samu tagomashi da farin jinin da ya yi dalilin zaɓen sa, domin ya hau mulki ya yi maganin ɓarayin gwamnati, masu yin gagarimar satar da ke hana Najeriya ci gaban da za ta bunƙasa ta zama mai ƙasaitaccen tattalin arziki.
Sai dai kuma kash, bayan Buhari ya shafe sama da shekaru bakwai kan mulki, har yanzu ‘yan Najeriya kan su a ɗaure ya ke. Sun kasa tantance shin wannan shin Buharin yanzu da ke yin wasu abubuwan da su ka raba hanya da mai halin yaƙi da rashawa, shi ne Buharin su na kafin zaɓen 2015 kuwa?
Daga tun da ya hau mulki bai nuna wani gagarimin hoɓɓasan kishin aikin da aka zaɓe shi don ya yi ba. Maimakon haka, sai ma ƙara jawo dandaƙaƙƙun ɓarayin gwamnati da waɗanda ake bincike da zargin gagarimar sata da Buharin ya riƙa yi a jikin sa, ya na yin bargon da ya ke lulluɓe jikin sa da su.
Kwatagwalcin Buhari: Bai Wa Bagudu, Tantagaryar Ɗan Kamashon Jidar Biliyoyin Sata Lambar Girma Ta CON:
Abin kwatagwalcin baya-bayan nan da Buhari gantsara wa kan sa da ‘yan Najeriya, shi ne bayar da lambar girma ta CON da ya yi ga Gwamna Abubakar Bagudu.
Banda Buhari da sauran ‘yan Najeriya, hatta duniya ta shaida irin yadda Bagudu ya zama direba, ɗan kamasho kuma dillalin lodi da jigilar biliyoyin dalolin da aka jida aka ɓoye ƙasashen waje, a zamanin mulkin marigayi Sani Abacha, wanda ya mutu cikin 1998.
An yi ittifaƙin cewa Abacha ya yi amfani da iyalan sa da makusantan sa irin su Bagudu, sun sace biliyoyin daloli daga baitilmalin Najeriya.
Daga 1998 zuwa yau, Najeriya ta karɓo dala biliyan 3.6 daga maƙudan kuɗaɗen da su Bagudu su ka kwashe su ka ɓoye ƙasashen waje a zamanin mulkin soja na Janar Abacha.
PREMIUM TIMES ta sha buga labarin cewa Gwamna Bagudu shi ne tantiri, tantagarya kuma gogarman lodi da saukalen maƙudan kuɗaɗen da su Abacha su ka riƙa karkatarwa zuwa ƙasashen waje a wancan lokacin.
Duk wannan daƙasharama, gadangarƙama, sabarƙala da asarƙalar da Bagudu ya yi a baya, babu wadda Buhari bai sani ba. Haka kuma Buhari ya san cewa a 2003 Bagudu ya amince maido wa Najeriya dala miliyan 163, don kada Amurka ta maida shi Jersey, lokacin da aka kama shi a Amurka ya yi zaman kurkukun watanni shida a can, saboda satar fitar hankalin kuɗaɗen Najeriya da aka kama ya yi.
Amma duk da haka, sai ga Buhari ya murje ido da kwalli, ya baɗa hoda, ya yi gazil ɗin canja wa ‘yan Najeriya fuska, ya ɗauki lambar girma ta CON ya bai wa Gwamna Bagudu. Abin takaici da kunya ga idon duniya, shi ne yadda aka ba shi lambar girma daidai da ta Amina Mohammed, Mataimakiyar Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), da kuma Ngozi Okonja-Iweala ta Bankin Duniya.
Lambar girma dai ko maras hankali ya san ana bayar da ita ne ga fitattun mutanen da su ka nuna kishi yi wa ƙasar su abin bajinta.
A wurin bayar da lambobin girmamawa ɗin, Buhari ya bai wa mutum 447, cikin su har da Bagudu, gogarman guduwa da maƙudan kuɗaɗen Najeriya.
Ƙarin abin kwatagwalcin da Buhari ya yi a ranar, shi ne a cikin waɗanda ya bai wa lambobin girmamawa ɗin har da Hadimin sa na Musamman, Sabiu Tunde, Kakakin Yaɗa Labaran sa Femi Adesina, Hadimin Harkokin Cikin Gidan Buhari, Sarki Abba, Likitan Buhari Sanusi Rafindaɗi, Sallaman Fadar Shugaban Ƙasa, Lawal Kazaure, Babban Jami’in Ayyukan Fadar Shugaban Ƙasa, Abubakar Maikano, surikin Buhari Sarkin Bichi, Nasir Bayero, da kuma ɗan uwan sa na jini, Mamman Daura.
Babu irin raddin da Buhari bai sha ba a ƙasar nan, tun bayan bayyana sunayen waɗanda za a bai wa lambobin girmamawa ɗin, har bayan damƙa masu lambobin.
Karsashi, Ɗarsashi, Tasiri Da Tagomashin Bagudu A Gwamnatin Buhari:
Baya ga kasancewar Bagudu shi ne Gwamnan Kebbi, kuma ɗan APC jam’iyyar su Buhari, shi ne kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC na Najeriya.
Bagudu ne shugaban shiga gaban tsayar da Bola Tinubu ɗan takarar shugaban ƙasa a APC a cikin watan Yuni. Kuma gogarma ne sukutum a cikin rundunar yaƙin neman zaɓen 2023 na Tinubu.
Masu gabatar da ƙara a Amurka sun gamsar da kotu hujjojin yadda Bagudu ya zama tsani da gadar da aka riƙa didima a kan ta ana sukuwar tserewa da kuɗaɗen Najeriya zuwa ƙasashen waje a zamanin mulkin Abacha. Kuma sun gabatar da hujjojin irin maƙudan kuɗaɗen da Bagudu da damfare a asusun banki daban-daban.
Sai da ta kai jami’an tsaron Amurka sun yi cacukui da shi, sun kulle shi a kurkuku tsawon watanni shida. Duk da irin wannan gadangarƙamar ba ta hana Bagudu zama gwamna a jam’iyyyar su Baba Buhari mai gaskiya ba.
Kafin ya zama gwamna, sai da ya fara yin sanata ma tukunna.
Tsakanin 1998 zuwa 2020, Najeriya ta karɓo kusan dala biliyan 3.6 daga ƙasashen waje, duk kuɗaɗen da iyalan Abacha da Bagudu su ka jida su ka ɓoye a ƙetare.
Duk waɗannan bayanan karɓo kuɗaɗen sata, PREMIUM TIMES Hausa ta riƙa bayar da labarin su dalla-dalla a baya. Ciki kuwa har da wata dala miliyan 308 da Najeriya ta karɓo daga Tsibirin Jersey, waɗanda kuɗaɗe ne da Bagudu ya sace, tsibe su can kan Tsibirin Jersey ɗin.
Shi ne kuma shekaru biyu bayan dawo da waɗannan kuɗaɗe sai Buhari ya bai wa wannan gazagurun ɓarawon gwamnati, kuma zamatoron jigilar kuɗaɗen sata lambar girma ta CON, gwarzon ɗan kishin ƙasar sa Najeriya.
Discussion about this post