Akalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu su sannan dukiyoyin mutane sun babbake bayan an kawo wutan lantarki mai ƙarfi a Gwargwaje da Kauran juli a Zariya jihar Kaduna.
Jami’in yada labarai na Kamfanin samarda wutan lantarki na Kaduna KEDC Abdulazeez Abdullahi ya sanar da haka wa manema labarai.
Abdullahi ya ce hakan ya auku ne yayin da tiransifoman dake barikin ‘yan sanda a Gwargwaje ya saki wuta mai ƙarfi.
Ya ce hakan ya auku ne a lokacin da wasu manyan wayoyin wutan lantarki suka harde da juna.
Dagacen Anguwan Malam Shu’aibu da barikin ‘yan sanda dake Gwargwaje, Bature Aliyu ya ce wutan lantarki gidaje da dama a yankin ya lalace sun koma suna zama cikin duhu a dalilin abin da ya faru.
Wannan abu ya yi sanadiyyar konewar shaguna da gidajen mutane da a ciki akwai gidan wani Zubair Abubakar.
Aliyu ya ce da dama daga cikin mutanen da gobarar ya shafa suna kwance a asibitocin gwamnati da kuma masu zaman kansu.
Shugaban hukumar kashe gobara ta Zariya, Umar Muhammad ya tabbatar da aukuwar abin da ya faru bayan jaje da ya aika wa mutanen da abin ya shafa.
Sarkin Zazzau Ahmad Bamalli ya aika da sakon ta’aziyar sa ga mutanen da suka rasa ‘yan uwansu a dalilin wannan ibtila’i da ya auku.
Sannan jami’in yada labarai na masarautar Abdullahi Kwarbai ya ce an gudanar da addu’o’In musamman Allah ya jikan wadanda suka rasu sannan ya kiyaye aukuwar haka a gaba..
Discussion about this post