Wannan Kogo ne da ke fidda ruwa wanda mutanen jihar Enugu ke zuwa domin neman waraka da rokon biyan bukata.
A lokacin da PREMIUM TIMES ta ziyarci wannan kogo mun iske mutane da dama, matasa da manya suna tururuwa zuwa wannan wuri.
Mutane kan tsindima cikin ruwan dake kwararrowa ta jikin duwatsu su yi wanka suna rokon biyan bukata, sannan kuma su ɗibi ruwan su ta fi da shi gida.
Wasu da suka tattauna da wakilin mu sun ce a wannan wuri ne mutane da dama suka boye a lokacin yaƙin Biafara. Sannan kuma mata masu neman haihuwa kan yi amfani da wannan ruwa domin samun biyan bukata.
Kogon Al’ajabi a jihar Enugu
Discussion about this post