Ita ma siyasa abace har halas, tana yin hukunci irin nata a siyasance. Ita fa siyasa ba kore ba ce a cikin duhu, kuma ba farautar kowa gaban sa bace.
Babu wani jagora da ya isa ya bunkasa a siyasa, sai da aminci, hakuri da jajircewar magoya bayan sa ba.
Duk yayin da jagora ya bunkasa ya zama wani, in har yaki yadda da ikon Allah a kan magoya bayan sa da abokan sa na siyasa, cika nasu burin, to sai ya rusa gidan sa kuma ya kansa kasa. Kafin na kai ga batu na, bari nayi wani tsokaci.
Tuna baya, Marigayi Abubakar Rimi da Malam Sule Lamido .
Allah ya gafarta wa Gwamna Rimi, bayan Aminu Kano har yau babu kamar sa a wannan yankin. Baya hassada a kan wani ya taka matakin da taka ba.
Ba dan Rimi ba, da Sule Lamido bai zama Chairman na banki ba, da Sule bai yi takarar Gwamna a SDP a 1992 ba, da baiyi takarar gwamana a 1999 ba, kai duk rawar da Sule ya taka, Rimi ne sila.
Hatta bunkarin G9 da tsohon Gwamna ke yi, na cewa mu muka kafa PDP, a tambaya aji, shin an yi G7 da su?
Marigayi Rimi ne ya sa Sule da mutane wani suka zama G9 da G7.
Rimi fa Gwamna kawai yayi, kuma bai taba kyashi ko bangarancin kadda wani na kasa da shi ya zama Gwamna ba.
A siyasa akwai Da, shi Dan na siyasa ba irin Danka bane, duk lokacin da a kayi watsi da yaya na siyasa, aka maida ta gado tamkar sarauta, wannan fa tamkar kisan kai ne a siyasa.
A tafiya ta siyasa samun mukami ba komai bane in har a kanfa gwamnati.
Ai baza a yi yaki da kai ba, kuma a maka gori don anyi rabon ganima da kai ba.
Wai ina wannan dakarun na Sule Lamido suke ne? mai ya sanya suka barshi a yanzu.
Wai ina Baban Beta, ina Danladi Sankara, ina Dr. Zama Fullata, ina Alhaji Ishak Hadejia, ina Baba Aminu Ringim, wai ina Ahmadu Kulkulin Gumel, ina Sabo Nakudu, Ina Alhaji Mammalon Katsina, ina su Malam Lawan Audu, ina su babana Jinjiri Dutse, ina su Arc. Aminu Kani, da sauran su.
Wai mai yasa duka suka watse suka bar Baba Lamido?
A duk wanda za a ce Da ne a wajen Sule, babu wanda ya kai Ahmadu, wannan ya tuna min wata magana ta Baba Sule “… Ahmadu masu gonar lema, kowa yazo PDP kai ya tarar……” amma yau ya haka? Domin babu wani Da na siyasa da ya kai Amb. Ahmed Abdulhamid a wajen Sule, amma bayan san ya taka sawun sa da shi da sauran, saboda sun fito daga wani yanki.
Ahmed yayi biyayya da kawaici ga maigidan sa Sule.
A takaice, a shekara 2007, dan takarar PDP a Jigawa Ahmed ne, bayan dawowar Saminu Turaki da mutanen sa daga ANPP zuwa PDP.
Sule Lamido bai taba tsayawa takara a kashin kansa ko jagorancin sa ya ci zabe ba.
Ko a 1999, bayan PDP taci zaben Shugabannin kananan Hukumomi 17 daga cikin 27 na Jigawa, sai gashi ya gaza kawowa PDP kujerar gwamanan. Ya tabbatar bazai ci zabe ba a 2003, sai yaki yin takarar, ya yaudari Baban Beta ya kaishi kasa, don ganin ya soma tagomashi a siyasa.
Sule Lamido ya jagoranci PDP a 2015, 2019, amma duka ya fadi warwas a Jigawa, kuma a bana ma faduwa zai yi. Saboda rashin adalchi na siyasa irin nasa.
Haka zalika, rashin iya jagoranci da adalchi na Sule Lamido, ya baza duk abokan siyasar sa na zahiri, domin baya son wani mutum ko wani yankin yayi gwamna, a 2015 ya maida takarar ga Aminu Ringim a baki amma a badini ya sare masa kafa kamar yadda yayi wa Baban Beta a 2003. Yau ina Malam yake?
Duk mai hankali ya kamata ya yi wa kansa hukunci, a duk yayan Sule na siyasa babu wanda ya chanchanta ya zama Gwamna sai Dan sa na cikin sa, mutumin koda monitor na aji bai taba yi ba, a danga masa ragamar mutane sama da miliyan biyar, duk kurin yan siyasar da ake cewa a kwai a PDP.
Ba munce Mustapha bazai yi takara ba ne, amma ya kamata a ce, anyi siyasar da mu’amala irin ta siyasa kamar yadda Baban sa yayi ya goge ya zamanto haka.
A yau babu wasu fitattun ya siyasa da suka rage a PDP daga tarkace, sai yan bana bakwai na Facebook, sai yan ritayar siyasa, duk saboda san rai da bangaranci na Jagora Sule.
Har gobe Ambassador Ahmed shi ke bin Sule bashi a siyasa, duk kololuwar da Sule ya kai a siyasa, su Ahmadu ne suka kafa da rike masa tsanin.
Amma in kuna san karin bayani ko jayayya a tambayi Malam Mammalon Katsina, ko uban kasa Obasanjo.
Duk maganganun Ahmadu na Sarawa babu kazafi, Sule Lamido akwai Yankin da baya so a Jigawa, kuma mutanen yankin sune gatan sa da madubin sa a siyasa har gobe.
Wannan halayyar ce ta sanya rushewar PDP a Jigawa, in har shi ne zai cigaba da jagorancin ta, sai an rasa kowa.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post