Ruɗani da hayagaga ya barke a taron jam’iyyar APC ta jihar Kano ranar Litinin, inda rahotanni suka nuna cewa har jinajina an yi a lokacin da rikici ya barke tsakanin ɗan majalisa Ado Doguwa da Ɗan takarar mataimakin gwamnan Kano na APC, Sule Garu.
Jaridar Daily Nigerian ta buga an kaure da faɗa ne tun daga farkon wannan taro.
A cewar jaridar, ana taron ƴaƴan jam’iyyar APC ne wanda ɗan takarar gwamnan jihar Nasiru Gawuna ya kira a gidan sa a Kano domin a yi bitar nasarorin da aka samu a lokacin ziyarar da kuma inda aka samu matsaloli a gyara su nan gaba.
An ce shidai ɗan majalisa Ado Doguwa ya halarci taron ne ba tare da an gayyace shi ba. Da ya isa wurin taron sai ya zarce wurin shugaban jam’iyyar Abdullahi Abbas, yana masa korafin me ya sa ba a gayyace shi ba
Sannan kuma ya zargi jam’iyyar da jefa shi a can baya a duk lokacin da aka zo tattauna magannan kuɗi amma idan aikin bauta ne shi ake tura wa gabagaba.
Majiya ta shaida wa jaridar cewa tunda farko Doguwa da Gawuna sun kaure da cacar baki ne l, inda yake zargin sa da saka ƴan barandan siyasa kada su saka hotunan sa a fostan kamfen a lokacin da Tinubu ya kawo ziyara jihar.
” Daga nan ne fa sai Suken Garu ya nemi ya jawo hankalin Doguwa da ya kwantar da hankalin sa da kuma yi masa tunin yadda ya rika sharara wa mahaifan sa ashar a taron jam’iyyar da aka yi a gidan Doguwan.
” Da bai gamsu da maganganun Garu ba, sai Doguwa ya wawuri kofin shayin mataimakin Gwamna Gawuna ya rankwala wa Garu, a kokarin tarewa da yayi da hannu sai da ya ji rauni a hannun.
Daga nan ne fa sai Gawuna ya fatattaki Doguwa sannan ya gargaɗe sa kada ya kuskura ya kara zuwa masa gida.
Rahotanni sun nuna tun bayan taron zuwan Tinubu garin Kano, Doguwa ya rika zazzabura, da farko dai ya dunkula babbar rigarsa ya jefi ɗan majalisa Ali Wudil wai don ba asaka hoton sa Tinubu ya gani ba, sannan kuma dama a baya ya kakkantara wa kwamishinan ƴada labarai na jihar Kano, Mohammed Garba rashin mutunci karara a wurin taro, sai kuma gashi ya rankwala wa Garu kofin shayi jar ay ji rauni.
Discussion about this post