Hukumar NDLEA reshen jihar Cross Rivers ta kama muggan kwayoyi da suka kai naira miliyan 200 daga watan Janairu zuwa Oktoba 2022.
Kwamandan hukumar na jihar Kupi Maulse ya sanar da haka ranar Litini a garin Calabar.
Maulse ya ce hukumar ta kama muggan kwayoyin da suka hada da hodar ibilis gram 77.9, hodar ibilis ta mai nauyin ruwa gram 104.9, methamphetamine gram 23.4, ganyan wiwi kg 162.52 da wasu kwayoyin dake saka maye da har kg 216.12 sannan jimlar su duka zai kai naira miliyan 50.
Ya ce hukumar ta kuma Kona gonakin wiwi guda biyu a dazukan Akamkpa da Odukpani masu fadin hekta 15 sannan kudin ganyen wiwin da aka noma ya kai naira miliyan 150.
Daga nan Maulse ya ce hukumar ta kama mutum 159 dake da alaka da sha ko safarar muggan kwayoyi a jihar.
Ya ce daga cikin wadanda suka kama kotu ta yanke wa mutum 21 hukunci, hukumar na gudanar da bincike akan mutum shida sannan sauran na jiran babban kotu a jihar ta yanke musu hukunci.
Maulse ya ce rashin isassun motocin sintiri na daga cikin matsalolin dake hana hukumar gudanar da aiyuka yadda ya kamata.
Ya ce masu safarar muggan kwayoyi na tallar muggan kwayoyi a fili, siyar da kwayoyin a bakin rafi da filayen kwallon kafa.
Sauran wuraren da ake siyar da kwayoyin sun hada da gidajen mutane musamman a tsofaffin unguwani, kofar kulub sannan da amfani da waya domin yin odar kwayoyin domin a kawo wa mutum har gida.
Discussion about this post