Babbar Kotun da ke Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja, ta yanke wa Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrashid Bawa, ɗauri a gidan kurkuku.
Mai Shari’a Chizoba Oji, ta umarci Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya ya garƙame Bawa a Kurkukun Kuje, saboda laifin raina kotu da ƙin bin umarnin kotu.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da tsohon Daraktan Gudanar da Ayyuka na Hukumar Sojojin Saman Najeriya (NAF), AVM Rufus Ojuao ya shigar, inda ya nemi kotu ta kama shugaban na EFCC, saboda ya ƙi bin umarnin kotun baya, wadda ta yanke cewa EFCC ta maida wa Rufus motar sa samfurin Range Rover, wadda aka ƙiyasta kuɗin ta zai kai Naira miliyan 40.
Tun a ranar 21 Ga Nuwamba, 2018 aka yanke hukuncin cewa a maida masa motar sa, amma a lokacin tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu.
Bayan Rufus ya fahimci Shugaban EFCC ya na raina wa kotu hankali, sai ya shigar da kara a neman masa haƙƙin sa, a kwafe lambar shari’a mai lamba FCT/HC/52/202.
Ganin yadda Shugabannin EFCC har zuwa Bawa sun ƙi bin umarnin kotu na saki sakin motar Rufus, a ranar Talata ɗin nan ce kotun ta umarci Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ya kama Bawa, ya kai shi Kurkukun Kuje.
Sai dai kuma yayin da PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Kakakin Yaɗa Labarai na EFCC, ya bayyana cewa ba su gamsu da hukuncin ba, za su ɗaukaka ƙara a gaba.
Discussion about this post