Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023 Atiku Abubakar, ya ƙudiri aniyar ɗaukar sojoji da ‘yan sanda miliyan ɗaya idan ya zama shugaban ƙasa.
Sannan kuma ya ce za a wadatar da su da ingantattun kayan aiki tare da ba su horo, domin samar da tsaro, aikin yi da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku ya yi wannan alwashin a lokacin da ya ke ganawa da shugabannin Kungiyar Editoci ta Ƙasa (NGE), a Legas, a ranar Laraba.
Ya ce wannan ƙudiri na cikin ajandojin sa biyar muddin ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023.
Ajandar sa ta biyu kuwa cewa ya yi ita ce farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa wanda kowa ya san ya taɓarɓare.
“Na ƙudiri aniyar ci gaba da irin tsarin da mu ka yi tsakanin 1999 zuwa 2007, lokacin ina mataimakin tsohon Shugaban Ƙasa. Za mu bai wa kamfanoni masu zaman kan su damar samun sauƙin ayyukan bunƙasa tattalin arziki.”
Daga cikin abin da zai yi wa kamfanonin, Atiku ya ce zai rage masu haraji ta yadda za su riƙa yin manyan ayyukan raya ƙasa, kamar gina tashoshin ruwa, manyan titina, hanyoyin jiragen kasa da sauran manyan ayyuka masu cin kuɗaɗe sosai, “musamman tunda gwamnati ba irin waɗannan maƙudan kuɗaɗe gare ta ba.
“Saboda daga Ni zan zaftare wa kamfanoni da masana’antu haraji, ta yadda su kuma za su riƙa gina manyan ayyukan raya ƙasa, waɗanda ke buƙatar kashe maƙudan kuɗaɗe kafin aikwatar da su.”
Atiku ya ce zai rungumi kowane yanki ba tare da nuna bambanci ko fifiko ba. Ya ce fifikon wani yanki da wannan gwamnatin ta riƙa bayarwa wajen raba muƙamai ba zai faru a gwamnatin sa ba, idan ya zama shugaban ƙasa.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna Aminu Tambuwal, mai suna Mohammed Bello ya fitar bayan ganawar, Shi kuwa Daraktan Kamfen ɗin Atiku/Yakuwa 2023, wato Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto, ya jinjina wa NGE da Ƙungiyar ‘Yan Jaridu ta Ƙasa (NUJ) wajen jajircewar su domin ganin dimokraɗiyya ta ɗore a ƙasar nan. Ya ce Atiku a shirye ya ke ya fara aiki wurjanjan da zaran an zaɓe ya zama shugaban ƙasa.
Discussion about this post