Ɗan takarar sanatan Kaduna ta tsakiya ƙarkashin jam’Iyyar PDP ya yi kira ga ƴaƴan jam’iyyar da basu ga maciji su hakura su zo a haɗa hannu gaba ɗaya domin samun nasarar jam’iyyar a zaɓe mai zuwa.
Usman Ibrahim da ka fi sani da sardaunan Badarawa, ya yi nasara a zaɓen fidda gwani wanda hukumar zaɓe ta kasa ta sake gudanarwa a garin Kaduna a cikin makon jiya bayan takaddamar da aka rika samu tsakanin sa da Lawal Adamu wanda aka fi sani da Mr La, kan wanene sahihin ɗan takarar kujerar na jam’iyyar PDP.
Idan ba a manta ba, tun bayan gudanar da zaɓen fidda gwani na farko da jam’iyyar PDP ta yi na kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya aka yi ta samun matsaloli, inda Sardaunan Badarawa ya ki amincewa da sakamakon zaɓen da yayi ikirarin an tafka maguɗi a ciki.
A dalilin haka ya garzaya kotu domin ƙalubalantar zaɓen. Daga baya kotu ta soke wannan zaɓe wanda Lawal Adamu yayi nasara a zaɓen ta ce a sake wani zaɓen fidda gwanin.
Ko da ya ke bangaren Lawal Adamu Mr La, sun kalubalanci hukuncin kotun da ta soke zaɓen tuni suka garzaya kotun ɗaukaka kara. Amma kafin haka sun ƙaurace wa zaɓen da hukumar zaɓe ta yi a Kaduna na sake zaɓen wanda zai cira tutar jam’iyyar a zabe mai zuwa.
Wani makusancin Mr La Kasim Bello, da ya tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA, ya bayyana cewa ba za su amince da hukuncin kotun ba kuma sai sun ga abinda ya ture wa buzu naɗi.
Sai dai kuma shi Sardauna, ya kaddamar da kamfen din sa a garin Giwa ranar Laraba, inda ya yi kira ga sauran ƴan PDP da suka fallo takubban yakin su cewa su maida su su zo a yi sulhu a samu haɗin kai don samun nasarar jam’iyyar a zaɓen 2023.
Gagarimin katangar karfe a gaban Sardauna
Ba a nan ne gizo ke sakar ba, Sardauna zai ci karo da rusheshen gungume a gaban sa a filin daga domin ba a PDP, a jam’iyyar APC akwai Matashin ɗan siyasa mai zamani, Mohammed Sani, daka fi sani da Dattijo wanda da shi za su fafata idan har kotu bata kwace takarar ba daga baya.
Koma dai wanene zai yi takarar, Dattijo na jiransa a filin daga.
Sardauna a ƙaramar hukunar Giwa
A wurin kamfen din sa da ya kaddamar a garin Giwa, Sardauna ya yi wa mutane alƙawalrin zai rangaɗa musu ayyukan cigaba da basu taɓa ganin irin su ba sanan zai rungume su a jika, ayi tafiya tare da kuma kwankwaɗan romon dimokuraɗiyyar akai akai.
Discussion about this post