Shin Yan Nijeriya suna da ma’auni da suke amfani da shi, wajen tantanche waya ya kamata su zaba wajen shugabancin su?
Shin Yan Nijeriya suna amfani da damar dimokaradiyya wajen nusar da shugabannin su, yayin da suka kasa sauke nauyi, akan muhimman al’amuran kasar su?
Kafin Shugaba Buhari ya samu nasarar zama Shugaban Kasa, yana gaba-gaba wajen nuna adawa a duk lokacin da a ka samu matsala a harkar da shafi Mayin Fetur a Nijeriya.
In muka yi karatun baya, a shekara ta 2014 a yayin campaign na zaben 2015, ya nuna cewa babu wani a bu Tallafin Mayin Fetur, kawai yaudarar yan Nijeriya gwamnatin da ke mulki ke yi.
Yace “Kawai a na yaudarar Yan Nijeriya a ke yi a kan Tallafin Mayin Fetur. Gwamnatin Tarayya kawai tana fitar da danyan Mayin Fetur ne ta taco shi a waje, ta dawo tana cewa za ta cire tallafi”
Ya kara da cewa “Wannan kawai shirme me ne da kuma yunkurin yan gwamnatin PDP don safe da kudin Kasa da sunan cire tallafin Mayin Fetur”.
Sai ga shi ba a je ko ina ba, bayan samun nasarar Buhari a shekara ta 2015, gwamnatin sa, ta dubulbule a kan matsalar Mayin Fetur, a 11 ga watan Mayu 2016 gwamnatin ta kara kudi litar mayin daga N87 zuwa N145 da sunan an cire tallafin.
Wani abin mamaki, duk da hakan sai gashi Gwamnatin Buhari a tsakanin shekara ta 2015-2018 ta kashe N1.2Tr a wajen bayar da Tallafin Mayin Fetur din.
A shekara ta 2019, gwamnatin ta kashe kimanin N2.3Trl kwatankwacin kashi 26% na kasafin kudin wannan shekarar, kuma kimanin kashi 17% na ajiyayyen kudin Nijeriya na waje (Foreign Reserve).
A karshen wannan gwamnatin, a kasafin kudin shekara mai zuwa 2023, an sanya sama da N3Trl domin bada Tallafin Mayin Fetur, wannan makudan kudade kawai na watanni 6 ne kachal, wanda in har gwamnatin gaba ta shigo ba ta da zabi, kafin ta samu gindin zama sai ita ma ta bada wannan kudi koma abin da yafi hakan zuwa karshen shekarar.
Duk da cewa Shugaba Buhari ya dau alkawura na kawo chanji da fasali a ma’aikatar Mayin Fetur, sai gashi matsalolin harkar Fetur kullum gaba su keyi.
A wannan shekaru da kasashe irin su Nijeriy masu arzikin Mayin Fetur ke cin gajiyar sa, saboda darajar sa a kasuwar duniya, Sai ga shi kullum tafka asara da kaka na kayi Nijeriya ke yi, saboda yawan satar danyan mayin da a keyi a koda yaushe.
A watanni bakwai kachal barayi da masu fasa bututun Mayin Fetur sun sace danyan mayin fetur na a kallah $10Bln a cikin watanni bakwai kachal.
Wannan kudin ya kai yawan kudaden da Nijeriya ke son ciyowa bashi da cike gibin kasafin kudin wannan shekarar.
Amma fa gwamnatin na kashe makudan kudade ga tubabbun yan ta’adda Niger Delter da a ka bawa kwangilar tsaron bututun.
A bangaren samarwa da gyaran matatun mayin fetur a karkashin wannan gwamnatin, babu wani abin a nuna.
Duk da cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta kashe N100B wajen gyaran matatun mayin fetur din kasar a shekara ta 2021, amma fa har yau basa aiki.
Ko da a bangaren yan kasuwa da masu sa jari, babu wani cigaba na a zo a gani.
Itama wannan gwamnatin kawai zance ne da jiran Dangote ya gama gina matatar mayin sa. Ko kuma lissafin Dokin Rano da jiran Gawon Shanu.
Shi kansa zargin cin hanci da rashawa a harkar Mayin Fetur bai ragu ba, sai dai a ce ma karuwa yayi.
A watan da ya gabata sai da shugaban hukumar Kwastan Col. Hamid Ali (Rtd) ya kalubalanci Hukumar NNPC akan cewa a kwai arangizon yawan litar mayin fetur din da suka ce suna shigowa da sayar da shi a Nijeriya, wanda karara ya nuna ayar tambaya da zargin rashawa a tsarin.
Dokar PIA, Petroleum Industrial Act, yunkurin yin dokar da za ta chanja fasalin kamfanin NNPC domin dacewa da zamani da kuma btakwarorin sa a duniya, abune wanda ya dau tsawon lokaci tun shekara 2000, lokacin mulkin Shugaba Obasanjo, samar da wannan doka kusan ya gagara.
Za a iya cewa a lokacin Shugaba Buhari ne a ka iya yin wannan doka amma dai har yanzu wannan doka a kasa bata kawo chanjin azo a gani ba, duk da samun komayyar da ta yi har sai biyu zuwa ga majalissar dokoki.
Za a iya cewa kawai a rubuce ne da karance dokar ta fi inganci.
Wannan karara ya nuna cewa dama tawagar Buharin, ba su da masaniyyar yadda harkar take, kuma ba suzo tsarin gyara a hannu su ba. Shi ya sanya shiga cikin wannan damaliya.
Ya kamata Yan Nijeriya suyi karatun ta nutsu wajen zaben shugabanni, in har muna son kawo gyara a tsarin tattalin arzikin Nijeriya.
Ya kamata Yan Nijeriya su fahimci cewa alkawura kawai ya zama abin da zai gamsar da mu ba.
Ya kamata duk mai son a zabe shi ya zo da jadawalin irin aiyukan da zai yi mana don kawo chanji.
Kuma dole sai mun tantance da nazari da kuma yarda da jadawalin.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post