Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana cewa rabon da a yi mummunar ambaliya a jihar kamar ta 2022, tun cikin 1936.
Kwamishinan Muhalli na Jihar Kogi, Vitor Omoyefe ya ce aƙalla ƙananan hukumomi 10 ne ambaliyar ta mamaye a halin da ake ciki.
Ya ce an samu asarar rayuka shida, yayin da a na ta ɓangaren gwamnatin jihar ta taimaka wajen rage yawan asarar rayuka ta hanyar saurin gargaɗin mutane su gudu da kuma kwashe wasu jama’a da aka riƙa yi zuwa yankunan da ke kan tudu.
Ya ce lamarin ya yi munin da zai iya cewa ya ma fi ƙarfin gwamnatin tarayya, don haka akwai buƙatar ƙasashen ƙetare da ƙungiyoyi daga waje su kawo ɗaukin gaggawa.
Victor ya ce, “rabon da a ga irin wannan ambaliya a jihar Kogi tun cikin 1936, inda ambaliyar sai ta ta kai ma’aunin ruwa 13.6 a shekarar.
“Amma ko ambaliyar 2012 ai ba ta kai ta yanzu ba, domin ta 2012 ai ma’aunin ta 12.8 ce. Ita kuwa ta yanzu ta kai 13.2,” inji shi.
Da ya ke ƙarin bayani, ya ce za a ci gaba da fuskantar ambaliyar a yanzu haka, domin tumbatsar da ruwan Kogin Neja da Kogin Benuwai ke yi su na haɗewa a Kogin Lokoja ke haddasa ambaliyar.
“Tilas idan ana so a samu sauƙin wannan ambaliya, sai an yashe yashin da ke Login Lokoja domin ya riƙa ɗaukar ruwa mai zurfin da zai daina kwarara cikin garuruwa da gonaki da dazuka,” inji shi.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa ambaliya ta ci rayuka fiye da 500, ta lalata gidaje 90,000, ta raba mutum miliyan 1.4 daga gidajen su a jihohi 31.
Gwamnatin Tarayya ta baya sanarwar cewa an yi mummunar asarar rayukan mutane 500, tare da lalata gidaje fiye da 90,000 a faɗin ƙasar nan, sanadiyyar ambaliya.
Ambaliyar wadda ta shafi jihohi 31, ta fi tsanani a jihohin Jigawa, Kogi, Kebbi da Bayelsa.
Babban Sakataren Ma’aikatar Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwar Marasa Galihu, Nasir Sani-Gwarzo ne ya tabbatar da waɗannan adadin alƙaluma, cikin ganawar da ya yi da manema labarai a ranar Talata, Abuja.
“Aƙalla fiye da mutum miliyan ɗaya ne ambaliya ta kora daga gidajen su, aka yi asarar rayuka 500, tare da samun wasu mutum 1,546 da su ka ji raunuka.
“Ambaliya ta yi wa gidaje 44,099 ɓarna, yayin da ta lalata wasu gidajen har 45, 249 baki ɗayan su.
“Aƙalla ruwa ya lalata amfanin gona a gonaki 76,168, yayin da wasu gonakin su ka lalace gaba ɗaya har guda 70,566 kwata-kwata.”
Sani ya ƙara da cewa masana da jami’an bincike sun tabbatar da cewa ambaliyar ta 2022 ta kai munin ta 2012.
Ya ce tuni Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta fara shirin raba kayan tallafi da agaji, wanda ya ce sama da mutane 315,000 ne za su ci moriyar agajin.
Discussion about this post