Kungiyar CS-SUNN ta bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna za ta bukaci akalla naira biliyan 6.4 domin kula da yara 96,488 dake fama da matsanancin yunwa a jihar.
Kodinatan kungiyar Jessica Bartholomew ta sanar da haka a lokacinda kungiyar ta kai wa gidan talabijin din KSMC ziyara a Kaduna.
Jessica ta ce daga cikin mutum miliyan 10 din dake zama a jihar Kaduna mutum miliyan biyu yara ne ‘yan ƙasa da shekara biyar.
Ta ce daga cikin su kashi 4.8% ko kuma yara 96,488 na fama da matsanancin yunwa a jihar.
Jessica ta ce daga cikin naira biliyan 6.4 din da ake bukata domin kula da yaran dake fama da yunwa gwamnati ta ware Naira biliyan 2.3 a kasafin kudinta na 2022.
Ta yi kira ga gwamnati da ta zage damtse wajen ganin ta ware isassun kudade domin inganta rayuwar mutane a jihar.
Bayan haka shugaban hukumar kasafin kudi da shirye-shirye na jihar Linda Yakubu ta bayyana cewa kungiyar CS-SUNN ta Kai wa KSMC ziyara ne domin karfafa kawancen da suka hada domin ci gaba da wayar da kan mutane mahimmancin ciyar da ‘ya’yan su abincin dake inganta garkuwar jikin su.
Linda ta ce gidajen jaridu na daga cikin muhimman kafofin da rika taimakawa akan wannan harkar.
Mataimakiyar shugaban fannin masana abincin dake inganta garkuwar jiki na jihar Adams George ta ce ganin yawan yaran dake fama da yunwa a jihar kamata ya yi a gaggauta daukan matakan ceto rayukansu a jihar.
Discussion about this post