Hukumar NDLEA reshen jihar Sokoto ta damke wani basarake dake harkallar muggan kwayoyi a jihar Sokoto.
Basaraken Umar Mohammed, shine dagacen kauyen Ruga dake karamar hukumar Shagari, Jihar Sokoto.
Da yake zantawa da manema labarai ranar Talata kwamandan hukumar Adamu Iro ya ce hukumar ta kama Mohammed bayan ta samu bayanan siri game da kwayoyi da ya ke harkallar su.
Iro hukumar ta dade tana neman Mohammed ruwa a jallo bisa ga laifin harkallar muggan kwayoyi da ake zargin sa da shi.
“Da farko mun kama matar Mohammed da kwayoyi amma sai muka sake ta bayan sakamakon binciken da muka yi ya nuna kwayoyin na mijinta ne.
“Amma Alhamdulillah ranar Litini mun kama Mohammed da tabar wiwi har kilogiram 436.381 da kwayoyin Diazepam a gidan sa.
Ya ce a hannun jami’an tsaron Mohammed ya ce ya dade yana harkallar muggan kwayoyi.
Iro ya ce hukumar za ta kai Mohammed kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.
Ya tabbatar cewa hukumar za ta ci gaba da farautar irin su Mohammed a gidan har zuwa wani lokaci sannan muna kira ga mutane da su cigaba da mara mana baya a wannan aiki da muka saka a gaba.
Haka kuma a wani rahoto da muka buka a cikin makon jiya jami’an NDLEA sun damke wani fasto mai suna Anietie Effiong da durum uku cike makil da hodar ibilis wacce suke kira Mkpuru Mmiri wanda aka yo masa safara sa daga kasar Indiya.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Legas Femi BabaFemi ya bayyana cewa an yi lodin kayan a mota kirar Bus daga unguwar Ojuelegba dake jihar Legas.
Discussion about this post