Kwamishinan Tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya gargaɗi masu shirin yin zanga-zangar datse titin Kaduna-Abuja zai kuka da kansa.
Wannan gargaɗi na kunshe ne a sanarwar da kwamishina Aruwan ya fid da ranar Talata a gare n Kaduna.
Kwamishina Aruwan ya ce ” Bisa ga kokarin da jami’an tsaro suke yi musamman a wannan lokaci na ganin an kawo karshen hare-haren ƴan bindiga a jihar musamman a wannan titi zanga-zangar da zai kawo cikas a hanyar zai iya maida hannun agogo baya.
” Saboda haka ana gargaɗin mutane da su nesanta kansu daga shiga cikin wannan gangami na shirin yin gudanar da zanga-zanga a kan wannan hanya.
A karshe ya bayyana cewa gwamnati ba za ta hana mutane gudanar da ƴancin su ba, sai dai kuma dole ayi komai bisa ka’ida da yin taka-Tsantsan a koda yaushe.
Discussion about this post