Kungiyar Ɗalibai ta kasa NAN ta bayyana cewa tun da safiyar Laraba zata datse titin Kaduna-Abuja domin zanga-zangar a kawo karshen yajin aikin ASUU da yaƙi yaƙi cinyewa.
A sanarwar zanga-zangar wanda kungiyar ta fitar ranar Laraba ta yi kira ga dukka kungiyoyin ɗalibai su fito kwansu da kwarkwata domin gudanar da tattakin da suka shirya.
” Muna kira ga duka kungiyoyin ɗalibai da su fito mu haɗu a titin Kaduna-Abuja a daidai Gonin Gora. Domin gaba ɗaya zamu datse hanyar ne babu wanda zai wuce a lokacin da muke zanga-zangar.
Sai dai kuma gwamnatin Kaduna ta gargaɗi kungiyar NANS kada su kuskura su gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihar saboda matsalar tsaro da ake fama da shi da kuma aikin fatattakar ƴan bindiga da ake yi musamman a wannan hanya.
Discussion about this post