Kansilan dake wakiltar Saminaka a ƙaramar hukumar Lere, jihar Kaduna Abubakar Sadiq ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya nada hadimai 32 a matsayinsa na kansila shine don ya saka wa waɗanda suke tare dashi.
A hira da yayi da DAILY NIGERIAN Sadiq ya ce ya nada wasu makusantan sa ne domin ya saka musu bisa goyon baya da suke bashi a siyasa.
” Babu abinda zai gagara, wadannan mutane ne da ke tare da ni a siyasa tun farko. Wannnan shine abu daya zan yi in saka musu. Da su muka yi Kamfen har muka yi nasara. Wannan shine abinda zan iya yi don saka musu.
Sadiq ya ƙara da cewa kula da su da dawainiyar su ba zai gagara ba.
Sadiq shine shugaban masu rinjaye a majalisar karamar hukumar Lere.
Discussion about this post