Jam’iyyar APC ta ƙi saka sunayen wasu jiga-jigan ta Kiristocin Arewa, waɗanda su ka fito fili su ka nuna rashin amincewar su da ‘yan takarar Muslim-Muslim.
Daga cikin waɗanda ba a saka cikin rundunar kamfen ɗin ba akwai tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara da kuma Sanata Elisha Abbo Mai wakiltar Adamawa ta Arewa.
Dukkan su ba su cikin Majalisar Kamfen ɗin Bola Tinubu na Zaɓen 2023.
An fitar da jadawalin sunayen a ranar Juma’a a dare, mai ɗauke da sa hannun Sakataren Majalisar Kamfen, James Faleke, wanda ɗan majalisar tarayya ne.
Shugaba Muhammadu Buhari ne zai zama Shugaban Rundunar Kamfen wadda ta ƙunshi mambobi 422 masu riƙe da muƙamai daban-daban.
A ranar Litinin ce za a ƙaddamar da rundunar a Abuja.
Babachir Lawal, Dogara da Tinubu dai duk sun goyi bayan Tinubu lokacin da ake zaɓen fidda gwani.
Sai dai kuma sun yi masa tawaye yayin da ya ƙi ɗaukar Kirista daga Arewa a matsayin Mataimakin shugaban ƙasa na takarar sa, sai ya ɗauki Musulmi, Kashim Shettima, sanata kuma tsohon Gwamnan Jihar Barno daga Arewa.
Su dogara sun jajirce cewa lamarin akwai rashin adalci, kuma an wulaƙanta Kiristocin Arewa.
Daga nan sun buɗe kamfen na tabbatar da cewa Kiristoci ba su zaɓi APC da Tinubu a zaɓen 2023 ba.
Haka nan ita ma Kungiyar Kiristoci ta Ƙasa (CAN) ba ta goyi bayan abin da APC ta yi ba.
Ko cikin wannan makon sai da Dogara da Lawan su ka yi kiraye-kirayen cewa kada Kiristoci su zaɓi APC, maimakon haka, su yi duk wani ƙoƙarin da za su yi su kayar da jam’iyyar.
Discussion about this post