An tabbatar da cewa ambaliyar da ta addabi Jihar Jigawa wadda ba a taɓa ganin irin ta a jihar ba, taci rayukan mutum 92 a jihar.
Adadin waɗanda su ka mutu ɗin dai an lissafa su ne tun daga lokacin da ambaliyar ta fara cikin Agusta har zuwa Satumba.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Jigawa Lawan Adam, ya tabbatar da cewa mamatan sun mutu ne sanadiyyar tafiyar- ruwa da wasu, wasu kuma a cikin kwale-kwale su ka kife a ruwa wasu kuma gini ne ko ɗakunan da su ke ciki ya ruguje da su.
Babban abin takaicin da ke damun al’ummar jihar da kewaye shi ne yadda Gwamna Abubakar Badaru ya tsallake ya yi tafiyar sa hutu a Turai daidai lokacin da ake tsakiyar fama da ambaliyar.
Sannan kuma ana kukan cewa har ya fitar ya bar ƙasar bai je kowane yanki ya yi ta’aziyya, jaje da alhini ba.
Ambaliyar ba jihar Jigawa kaɗai ta shafa ba, ta shafi matafiya zuwa Bauchi, Yobe, Barno da sauran jihohin Arewa maso Gabas, sanadiyar karyewar wasu gadoji da ke kan titi da kuma zabtatewar kwalta saboda ruwa ya zaizaye wasu wuraren.
Dubban ‘yan jihar waɗanda ambaliyar ta shafa na zaune a sansanonin masu gudun hijira, yayin da aka kulle makarantu a jihar.
Badaru ya aika wa Majalisar Dokokin Jigawa wasiƙar cewa zai lula hutun sati biyu, tun daga ranar 7 Ga Satumba, zuwa 22 Ga Satumba.
Jama’a da dama na ƙorafin cewa Gwamnatin Jigawa da Gwamna Badaru sun yi watsi da waɗanda ambaliyar ta shafa, ba a yi masu wani tallafin a zo a gani ba.
Naira miliyan 50 ɗin Bola Tinubu ya bayar tallafi lokacin da ya je jaje, bai isa hana al’ummar jihar ci gaba da ƙorafi ba.
A makon jiya ne kuma Sanata Danladi Sankara ya bayar da tallafin kuɗi Naira miliyan 20, buhunan shinkafa 2,000 da sauran kayayyaki a yankin sa, domin rabawa ga waɗanda ibtila’in ambaliya ya shafa.
Discussion about this post