Tabbas duk al’umar da baza su iya kare tarihin su ba, tamkar rashin sanin kai ne da hangen nesa. Duk al’umar da bata da tarihi tabbas lokaci zai shafe shi.
Wadannan hotunan kusan abubuwan da suka rage kenan a gineginen turawan mulkin mallaka a garin Hadejia.
A yau ba a maganar ganuwar da ta kewaye garin na Hadejia, duk da kasancewar Kasar Hadejia da garin Hadaejia sannan ne a a fadin kasar hausa, labarin tarihin su da jaruntar ya kewaya duniya, har ya zama abubuwan da a ke bincike a kan su a makarantu da masu neman ilimi.
Manyan garurwu tsarar Hadejia hatta ganuwar da ta kewaye garuruwan su sun killace ta da kare ta domin tabbatar da tarihin su, amma a nan hankoran mallakar filotai don arzuta kai. Mayar da Filin gina gida ya zama kaddara wannan tasgaro ne na ilimin tattalin arziki.
Hadejia tayi kaurin suna a fadin duniya, fitatttun mutane a duniya su kan zo Hadejia don gani da ido, saboda tasirin da Hadejia tayi a tarihin duniya.tarihin bahaushe da Bayajidda baya cika sai ka sanya Hadejia da Biram ta Gabas
Tarihin yaki da gwagwarmayar da aka yi da Hadejiyawa lokacin mamayar turawan mulkin mallaka, wanda wannan gwagwarmaya da jajircewar Hadejiawa ya sanya turawan Ingila suka sanya Hadejia a cikin tarihin su na mulkin mallaka.
Mr. Philips wanda a ke kira da Maitunbi, shine Baturen da ya jagoranci turawan Ingila mamayen Hadejia a 1903, wanda a wannan lokacin basu samu nasara ba, ya koma garin Katagun da ke Jahar Bauchi a yau, kafin da ga baya ya sake dawowa Hadejia a shekara ta 1904.
Kafin turawan mulkin mallaka su sami galabar mamaye Hadjia, sai da a kayi gumurzu da yaki mai tarihi, a wannan yakin ne aka kashe Mr. Philips (Maitumbi), turawa sun binne shi a nan kuma suka sanya alama a kabarin sa, wanda daga baya mutane suke rushe wannan kabarin na Maitunbi.
Madallah da kokarin da Dan Masanin Hadejia yayi, President na ICAN Alhaji Tijjani Musa, wanda ya gyara kabarin da kuma killace shi. Wannan ba karamin gudunmawa bane don kare martabar Hadejiada kuma kare tarihin ta.
A lokacin mulkin mallaka Hadejia ta kasance Lardi wadda Larduna irin su Katagun wato Azare, Gumel, Kazaure duka suna karkashin Lardin Hadejia ne.
Yayin da kasashen da suka ci gaba dama jahohin suke killacewa da adana kayayyakin tarihin su hatta alamomi da diddgen kayayyakin yan mulkin mallaka don ilmantar da da mutane masu zuwa.
Yau a cigaba ma na zamani abubuwa na tarihi sun zamanto hanyoyin bukasa tattalin arziki ta hanyar yawan bude idanu, amma a irn wannan yanki namu rusa su ma mukeyi don biyan karamar bukata ta kayuwan mu.
Rusa kayan tarihi don mallakar fili ko foloti don gina gda a irn garin Hadejia mai isashen kasa da za a iya gina muhallai, ba karamin toshewar basira bace a ce irin wdannan wurre a ke rusawa da mallakawa wasu mutane.
Wadanna hotuna gine gine ne tun na turawan Birtania na mulkin mallaka da offisoshin su, amma abin takaici wanan gine gine da ma filayen wanan gidajen an barsu suna reshewa.
Babban abin damuwar shine yadda gwamnati ta kekketa wuraren ta rabarwa wasu mutane da ban domin gina gidaje, wanda a nan gaba wanna wurin zai shafe, ya zamanto babu komai.
Tabbas wannan mataki da gwamnati ta dauka da duk masu hannu a ciki na rusa tarihin Hadejia, Nigeria da Ingila ba karamin kalubale bane a wannan zamanin da ma wanda zasu zo a gaba.
Ya kamata gwamnatin Jahar Jigawa da manyan masarautar Hadejia su duba wannan al’amari na yankawa da rarraba wannan filaye. Ya kamata a killace su a inganta su domin masu zuwa yawan bode ido da ma masu neman tarihi.
Amma wannan mataki tamkar nunawa duniya ne rashin sanin kai da kishin al’umar su.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post