Yayin da ake fama da matsalar wutar lantarkin da ta ci ta ƙi cinyewa a Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yawan maida hankali da ake yi wajen samar da wutar lantarki ta hasken rana, wato sola, zai kai Najeriya wajen ƙara samar da wuta ga yankunan da ba ta wadace su ba, har ma da yankunan da ba su taɓa samun wutar lantarki ɗin ba.
Buhari ya yi wannan bayani a Abuja, yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar kamfanin SUN Africa LLC, USA, waɗanda su ka kai masa ziyara.
Ya ce gwamnatin sa ta bijiro da shirye-shirye masu yawa da alfanu domin farfaɗo da harkokin wutar lantarki a Najeriya, cikin garuruwa, birane da yankunan karkara.
Ya jinjina wa yadda kamfanin samar da wutar sola na Amurka, ganin yadda ya maida hankali wajen samar da hasken wutar sola a yankunan ƙasar nan.
Buhari ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da bayar da haɗin kai ga kamfanoni masu zaman kan su wajen ganin an inganta wutar lantarki a yankunan ƙasar nan daban-daban.
Buhari ya karanto masu wasu daga cikin ayyukan bunƙasa harken lantarki da ya ce gwamnatin sa ta yi.
Sai dai kuma a wani labarin kan matsalar wuta, Kamfanonin Raba Wutar Lantarki sun yi fatali da shirin yi masu garambawul, sun ce su na bin gwamnati bashin naira biliyan 100.
Ƙungiyar Kamfanonin Raba Wutar Lantarki a Najeriya (ANFD) ta yi fatali da shirin da Gwamantin Tarayya ke yi domin yi kamfanonin raba wuta wato DisCos garambawul a faɗin ƙasar nan.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa gwamnati ta kasa cika alƙawarin da ta ɗauka na biyan su kuɗaɗen tallafi da sauran alƙawurran da aka ɗaukar masu tun 2013. Sun ce adadin kuɗaɗen da su ke bin gwamnati ya kai naira biliyan 100.
Babban Daraktan Bincike Sunday Oduntan ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar, kuma ya sa mata hannu.
Aƙalla dai kamfanonin DisCos biyar ne bankuna su ka karɓe, saboda sun kasa tabuka komai bayan sun ramci maƙudan kuɗaɗe a bankunan.
Wannan kamfanonin raba wuta da bankuna su ka ƙwace wa asusun tara kuɗaɗe kuwa sun haɗa da Abuja DisCo, Benin DisCo, Ibadan DisCo, Kaduna DisCo da kuma Kano DisCo.
Kwanaki kaɗan bayan Hukumar Kula da Wutar Lantarki (NERC) ta sanar cewa harkar samar da wuta za ta koma bisa ƙa’idar kwangila, kamfanonin raba wutar lantarki su kuma sun ce idan aka yi haka, lamarin matsalar wuta zai ƙara muni a ƙasar nan.
Sannan kuma sun ja hankalin gwamnati da cewa idan ta shigo da wannan tsarin, to fa ta karya yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin Hukumar Sayar da Hannayen Jari ta Ƙasa (BPE) da kuma NERC.
NERC da BPE sun ce za a sayar da mafi yawan hannayen jarin da ke cikin kamfanonin DisCos ga ‘yan kasuwa masu sha’awar zuba jari, waɗanda za su iya narka uwar kuɗaɗen da za su tafiyar da harkokin kasuwancin wutar lantarki da gaske.
Gwamnatin Tarayya ta ce bankin Fedility ya nuna amincewa zai shiga dukkan harkokin kasuwancin da za a inganta wutar lantarki, ciki kuwa har da Shirin Samar da Mita na Ƙasa.
Sai dai kuma kamfanonin raba wutar lantarki (DisCos) sun ce tunda gwamnati ta kasa cika yarjejeniyar da BPE da NERC su ka ƙulla, to ta na da hannu wajen kasa taɓuka komai da ake zargin kamfanonin raba wuta sun yi.
Sun ce “ƙoƙarin yi wa kamfanonin garambawul ɗin da gwamnati ta ce za ta yi, ya saɓa da ƙa’idoji da yarjejeniya da kuma dokar ƙasa.”
Sun ce idan har gwamnati ta yi abin da ta ce za ta yi, wato garambawul ɗin, to kawai ta maida su hannun hukuma kenan, daga hannun ‘yan kasuwa a fakaice.
Najeriya dai na ci gaba da fama da matsalar wutar lantarki, inda a cikin 2022 babbar tashar samar da wuta ta durƙushe sau takwas.
Discussion about this post