Babban Kotu dake jihar Ekiti ta yanke wa Oladipupo Seun mai shekara 40 hukuncin zaman kurkuku na tsawon shekaru 16 bisa zargin aikata laifin kokarin yi wa ‘yar shekara 18 fyade da cin zarafin ta a gidan mahaifin ta.
A kotun Seun ya ce shi bai yi kokarin yi wa yarinyar fyade ba domin yarinyar budurwarsa ce.
Ya ce wasa da juna ne kawai suke yi suna ɗan taɓe-taɓe a lokacin da mahaifinta ya shigo ɗakin da suke ya gansu.
Alkalin kotun Adekunle Adeleye ya ce ya yanke wannan hukunci ne bisa ga shaidu da hujjojin da aka gabatar a kotun da suka tabbatar cewa Seun ya aikata laifin da ake zarginsa da shi.
Lauyan da ya shigar da karar Folasade Alli ya ce Seun ya aikata wannan ta’asa ne ranar 19 ga watan Faburairun 2021 da misalin karfe 11 na dare a gidan yarinyar dake Igede Ekiti a karamar hukumar Irepodun/Ifelodun.
Alli ya ce a wannan dare Seun ya je gidan yarinyar ba tare da ta gayyace shi ba sannan daga shiga dakin yarinyar sai ya mamayeta ya hada ta da bango ya toshe bakinta yana kokarin yi mata fyade.
“Yana cikin yin haka ne mahaifin yarinyar ya shigo dakin daga nan sai Seun ya fece.
Lauyan ya gabatar da shaidu da hujojin inda a ciki akwai sakamakon gwajin da aka yi wa yarinyar da bayanin da yarinyar ta yi wa ‘yan sanda da suka tabbatar cewa Seun ya yi kokarin yi mata fyade.
Lauyan dake kare Seun, Helen Akinboni ta musanta haka inda take cewa yarinyar budurwar Seun ce sannan mahaifin yarinyan ya shigo ya kama su suna wasa da juna.
Helen ta ce Seun ya gudu ne saboda ya ji tsaron abin da mahaifin budurwar ta sa zai yi masa a wannan lokaci.
Discussion about this post