Sojojin Najeriya sun tabbatar da kashe manyan ‘yan ta’adda da dama a yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Babban Hafsan Sojojin Sama Oladayo Amao ne ya yi wannan albishir ranar Talata a Abuja, a wurin wani taro.
Ya ce wasu hare-haren sama da aka riƙa kai wa ‘yan ta’adda a sama da kuma ta ƙasa ya haifar da samun nasarar da aka yi, ta dalilin gamayyar taron dangin da aka yi wa ‘yan ta’addar.
Daraktan Yaɗa Labaran Rundunar Sojojin Sama, Edward Gabwet ne ya tabbatar da haƙa.
Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa ce ta shirya taron, wato NOA.
“Mun yi imanin cewa gamayyar da mu ka yi da sauran ɓangarorin tsaro zai ci gaba da tasiri na tsawon lokaci wajen daƙile duk wata barazanar tsaro a ƙasar nan.
“Wannan ƙoƙarin da haɗaka da mu ka yi kuma babu shakka ya samar da gagarumar nasara.
“Saboda an samu gagarimar nasarar karkashe manyan ‘yan ta’adda da dama a yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya.” Inji shi.
Ya ƙara da cewa Sojojin Sama sun riƙa bin mutane su na yi masu ayyukan kula da lafiya, inda kimanin mutum 400,000 su ka amfana.
Hakan, a cewar sa ya na cikin ƙoƙarin ƙara kusantar juna ne tsakanin sojojin da farar hula.
Discussion about this post