Dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar NNPP, jam’iyya mai alamar kayan dadi, Suleiman Hunkuyi ya bayyana cewa idan jam’iyyar sa ta yi nasara a zaben gwamnan jihar Kaduna, zau sauya duk canjecanjen da El-Rufai yayi wa fasalin aikin gwamnatia jihar Kaduna.
” Abin da zan fara yi idan na zama gwamnan Kaduna shine zan dawo da duka masarautun da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya rushe su, wato masarautu sama da 300.
” Sannan kuma zan soke karin kudin makaranta da gwamnatin tayi musamman na manyan makarantun jihar saboda talakawa su samu damar saka ya’ayn su a makarantun jihar.
Hunkuyi ya dade yana takarar gwamman jihar Kaduna inda a dalilin haka ya tsindima cikin kusan duka manyan jam’iyyun kasar nan amma Allah bai sa ya cimma buri ba.
Ya ce gwamnatin idan Allah ya bashi sa’a zai rungumi jama’a ne kusa sannan ya zai tabbatar talaka ya kwankwadi romon dimokradiyya, bai yi da na sani ba.