Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Tarayya, Babajimi Benson (ɗan APC daga Jihar Legas), ya nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tunanin tattago sojojin haya daga ƙasashen waje, domin a magance matsalar tsaron da ke ƙara muni a ƙasar nan.
Benson ya yi wannan kiran a ranar Juma’a, lokacin da ake tattaunawa da shi a gidan Talbijin na Channels.
Ya ce duk da ya gamsu da yadda Buhari ya sha nuna rashin goyon bayan tattago sojojin haya, kasancewa Buhari na da ƙwarewa ta aikin soja, Benson ya ce a yanzu lamarin tsaro ya yi munin da babu makawa dai an ɗauki matakai masu tsaurin gaske kafin a shawo kan matsalar.
Alaƙar Najeriya da Sojojin Haya:
Cikin 2015, gwamnatin Goodluck Jonathan ta tattago hayar sojojin haya daga Afrika ta Kudu, waɗanda su ka ƙware wajen iya bada horo, dabarun sarrafa makamai da kuma sha’anin bada kariyar tsaro, su ka yi faɗa da ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas.
Daidai lokacin da zaɓen 2015 ya kusanto, Buhari ya riƙa sukar gwamnatin Jonathan saboda alaƙar ta da sojojin haya wajen yaƙi da Boko Haram.
A wata ganawa da Buhari ya yi kafin a rantsar da shi tare da Kungiyar Dattawan Arewa (ACF), Buhari ya ragargaji gwamnatin Jonathan cewa alaƙar da ta ke yi da sojojin haya, abin kunya ne fitik.
“Babu babban abin damuwa kamar yadda Sojojin Najeriya za su koma sai sun yi amfani da sojojin haya kafin su samu wannan nasara da su ka samu kan Boko Haram. Wannan lamari abin kunya ne.” Inji Buhari a lokacin Jonathan.
A kan harin jirgin ƙasa a hanyar Kaduna kuwa, Gwamnan Kaduna kuma makusancin Shugaba Buhari, ya ce idan gwamnatin tarayya ba za ta iya kakkaɓe ‘yan bindiga daga dazukan Arewa maso Yamma ba, “to gwamnonin yankin za su ɗauko hayar sojojin haya daga ƙasar waje kawai.
“Na yi wa Shugaban Ƙasa ƙorafin halin matsalar tsaro da ake ciki. Kuma na rantse idan idan aka kasa yin komai, to mu gwamnoni za mu ɗauko sojojin haya a yi ta ya ƙare.”
Aikin Da Aka Ɗirka Wa Sojoji Ya Yi Masu Yawa -Hon. Benson
Da ya ke kawo hujjar da ya ce idan gara a kawo sojojin haya, ya ce ayyukan da aka ɗora wa sojoji ya sha kan su sosai a faɗin ƙasar nan.
Ya ce akwai guraben da sojojin haya za su cike. “Idan ni ne shugaban ƙasa, sai na ɗauko sojojin haya kawai. Ya kamata a duba a gani, ayyukan da ke kan sojoji sun yi masu yawa. Sojojin Najeriya na aiki a cikin jihohi 35 na ƙasar nan.” Su na buƙatar kawo ɗauki daga ‘yan sanda da jami’an tsaro na NSCDC.
Discussion about this post