Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku ta Ƙasa Haliru Nababa, ya bayyana ƙarara cewa ba a gina Kurkukun Abuja da ke Kuje da nagartar jure dafin rugugin manyan malaman Boko Haram ba.
Nababa ya yi wannan furucin a lokacin da ake wata doguwa kuma zazzafar tattauna makomar tsaro a gidajen kurkukun Najeriya, wanda PREMIUM TIMES ta jagoranci tattaunawar a shafin ta na Tiwita, a ranar Litinin.
A cikin tattaunawar wadda aka shafe fiye da sa’o’i biyu, an yamutsa gashin baki da manyan masana harkokin tsaro da sauran su a shafin tiwitar.
Nababa ya ƙara da cewa wasu daga cikin matsaloli ko ƙalubalen da Gidajen Kurkuku ke fuskanta shi ne matsalar manyan makamai.
“Sannan kuma jami’an tsaron mu ba su da manyan bindigogi irin waɗanda Boko Haram su ka kai wa Kurkukun Kuje hari da su.”
Da ya ke magana kan rashin yin amfani da rahotannin sirri na ‘yan leƙen asiri kuwa, Nababa ya ce tabbas an samu rahotannin sirrin akwai alamomin za a kai hari a yankin. “Amma ba gaskiya rahotannin ba su ce takamaimai ga wurin da za a kai harin ba. Kuma ba a ce hususan a Kurkukun Kuje za a kai harin ba.”
Haka kuma ya ce jami’an tsaron Gidan Kurkukun Kuje sun yi kaɗan ɗin da za su iya tarar-aradun jure farmakin Boko Haram, a daren da su ka dira kurkukun.
Nababa ya ce “Gidan Kurkukun Kuje ya na ɗaukar ɗaurarru 3,000. Amma ba a gina bangon gidan don jure rugugin wutar da Boko Haram su ka buɗe a ranar Talatar da su ka kai harin ba. Kai ko bindigogin mu ma ba su iya gogayya da manyan bindigogin Boko Haram.” Inji Nababa.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda ISWAP su ka raba wa ɗaurarrun da su ka kuɓutar daga Kurkukun Kuje Naira 2,000 kowa ya yi kuɗin mota zuwa gida
Mazauna garin Kuje, musamman waɗanda ke kusa da kuma bayan kurkukun da aka kai wa hari, sun bayyana wa wakilin mu yadda lamarin ya faru, wanda su ka ce ba su fatan su ga maimaicin wani abu mai kama da haka.
Farmakin wanda aka kai a ranar Talata, ya yi sanadiyyar arcewar ɗaurarru 800 daga cikin mutum 994 da ke tsare su a ciki.
Sai dai kuma jami’an kurkukun sun ce an kamo 442, amma kuma har yanzu babu labarin sauran 443 da su ka tsere.
Wani maƙaucin kurkukun mai suna Micheal, ya shaida wa wakilin mu cewa maharan aƙalla za su kai 100.
Ya ce ba garkiya ba ne da gwamnati ta ce kimanin minti 30 maharan suka yi.
“Gaskiya sun fi awa biyu a kurkukun. Saboda tun ƙarfe 9 na dare su ka dira, kuma 11 su na wurin.
“Ni ina ƙofar gida tare da wani aboki na, mu na shirin hawa babur mu je wani wuri, wajen ƙarfe 9 na dare, kawai sai mu ka fara jin ƙara da rugugi. Ni da farko na yi zaton ko nakiya ce ake fasawa ma. Wannan ƙarar rokoki ne da aka riƙa harbawa don a fasa bangon kurkukun.”
Micheal ya ce da ya ga abin ba na wasa ba ne, ya dafe ƙeya ya shiga gida a guje.
“Na nufi gida a guje. Wani soja daga cikin waɗanda ke gadin kurkukun ya biyo ne shi ma a guje, mu ka runtuma mu ka afka cikin gida. Sojan nan ya yi sauri ya cire yinifom ɗin sa. Mu ka shige ƙarƙashin gado.”
“Bindigogin da maharan ke amfani da ita, manya ne sosai, kuma da harsasai kawai ke fita, ba ƙaƙƙautawa.”
Wani kuma da aka zanta da shi, ya ce sun ga yadda ɗaurarru su ka riƙa fita su na tserewa.
“Wasu ma tafiyar taƙama su ke yi abin su. Wasu kuma gudu wasu sauri.
“Maharan sun riƙa raba wa waɗanda su ka tsere ɗin kowane naira 2,000 domi ya yi kuɗin mota. Wani wanda ya kasa tafiya ne da ya ga ba zai iya ba, wataƙila saboda rauni, ya shaida mana haka. Har ma ya yi ƙoƙarin maida naira 2,000 ɗin da ya ce an ba shi.”
Ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun tsallako rafi ne su ka kai harin.