Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola ya bayyana cewa akwai sama da ‘yan ta’adda 61,000 da sauran miyagu makamantan su da ke tsare a magarƙama daban-daban a jihohin Arewa maso Gabas na Najeriya.
Aregbesola ya yi wannan iƙirarin ne a lokacin da ya kai ziyarar duba Kurkukun Kirikiri da ke Legas.
Cikin ziyarar wadda ya kai a ranar Talata, kamar yadda Kakakin Yaɗa Labaran sa, Sola Fasure ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
Yaƙin Boko Haram dai ya ci rayukan sama da mutum 100,000 a yankin Arewa maso Gabas.
Aregbesola ya bugi ƙirjin cewa, “Gwamnati ta dakile ta’addancin Boko Haram. A yanzu haka akwai ‘yan Boko Haram da sauran masu aikata laifin irin na su har mutum 61,000 da ke tsare a magarƙamu daban-daban a yankin Arewa maso Gabas. Saboda haka za mu ƙarasa kakkaɓe ɓurɓushin da su ka rage.”
Aregbesola ya yi wannan maganar mako ɗaya bayan mummunan harin da Boko Haram su ka kai wa Kurkukun Kuje, inda su ka kuɓutar da ‘yan uwan su har 64 da ke tsare a ciki.
Wannan jarida ta buga labarin cewa fiye da fursunonin 4,300 ne su ka arce daga gidajen kurkukun Najeriya, tsakanin 2017 zuwa 2022.
A labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya gargaɗi Shugabannin Tsaro cewa kada su sake ko da mutum ɗaya ya sake tserewa daga gidajen kurkukun Najeriya.
Haka kuma ya ce ba zai sake lamuntar su bari a sake kai hari a kowane gidan kurkuku ba.
Buhari ya yi wannan gargaɗin bayan Boko Haram sun kai wa Kurkukun Abuja da ke Kuje hari a ranar Talata, inda fiye da ɗaurarru 800 su ka arce, ciki har da riƙaƙƙun ‘yan Boko Haram 64 da ake tsare da su tsawon shekaru da dama.
Buhari ya bada wannan umarni a wani Taron Majalisar Tsaro da ya yi a Fadar Shugaban Ƙasa, Aso Rock Villa, Abuja a ranar Alhamis.
Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Maigari Dingyaɗi ne ya bayyana wa manema labarai gargaɗin wanda Buhari ya yi.
An dai kai harin ne a ranar Talata, rana ɗaya da aka kai wa tawagar hadiman Buhari harin kwanton ɓauna a Dutsinma, kan hanyar su ta zuwa Katsina.
“Shugaban Ƙasa ya nuna ɓacin ran sa sosai. Kuma ya gargaɗi Shugabannin Tsaro su tabbatar sun ɗauki ƙwararan matakan da ba su bari an sake kai wa gidajen dursunoni hari ba.”
Dingyaɗi ya ce kuma Buhari ya gargaɗe su kada su bari ko mutum ɗaya ya sake tserewa daga gidajen kurkukun faɗin garuruwan ƙasar nan.
Aƙalla dai fursunoni 4,307 ne su ka tsere daga gidajen kurkuku daban-daban daga 2017 zuwa 2022.
Cikin Afrilu 2021 fiye da ɗaurarru 1,800 su ka tsere daga Kurkukun Owerri na Jihar Imo.
A cikin watan Nuwamba kuma aka kashe mutum 10, ɗaurarru 252 su ka arce daga Kurkukun Jos.
Kafin nan kuma cikin Oktoba ne mutum 837 masu jiran a yanke masu hukunci su ka tsere daga Kurkukun yarin Oyo.
Discussion about this post