A cikin daren Talata ne wasu ƴan bindiga da ake zaton ƴan Boko Haram ne duka yi kukan kura suka far wa gidan yarin dake Kuje suka tada bamabamai har hudu sannan duka kutsa ciki.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun dira Kuje ne domin kuɓutar da wasu ƴan bindigar ga da ake tsare da su a wannan gidan yari.
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ƴan bundigan sun dira Firzin ɗin kuje ne da misalin karfe 10 na dare.
Bayan sun isa sai suka jejjefa bamabamai har guda huɗu a duka kofofin shiga harabar gidan yarin. Daga nan sai suka fara buɗe wuta da manyan Bindigogi suna kabarbari.
An bada rahoton cewa akwai wasu mashahuran ƴan bindiga da Boko Haram da gwamnati ta tsare su a wannan gidan yari wanda a cikin makon jiya ne aka kawo su Abuja.
Discussion about this post