‘Yan bindiga sun yi wa tagawar hadiman Shugaba Muhammadu Buhari kwanton ɓauna, inda su ka raunata mutum biyu, saura su ka tsira.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Buhari, Garba Shehu ya tabbatar da kai harin a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Talata.
Shehu ya bayyana cewa harin da aka kai wa tawagar abin baƙin ciki ne.
Tawagar dai ta afka cikin mahara ‘yan kwanton ɓauna kusa da garin Dutsinma mai nisan kilomita 64 tsakanin sa da Katsina.
Su na kan hanyar su ne ta zuwa Daura domin su riga Buhari isa garin, inda zai je domin ya yi hutun Babbar Sallah a can.
Tawagar dai ta ƙunshi jami’an tsaro, hadiman kai-da-kawo da jami’an yaɗa labarai.
“Mahara sun buɗe wa tawagar wuta daga inda su ka yi kwanton ɓauna. Amma sojoji, ‘yan sanda da DSS sun kore su.
“Mutum biyu a cikin tawagar sun samu raunuka. Saura kuma sun isa Daura lafiya.” Inji sanarwar.
An dai kai wa tawagar hari a yankin da rahotanni daga Katsina ke nuna cewa ‘yan bindiga sun kashe Kwamandan ‘Yan Sandan ‘Yankin Dutsinma, wato Area Commnder, wanda Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda ne.
Discussion about this post