Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, Bola Tinubu ya kai ziyarar bazata fadar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo.
Tinubu ya kai ziyarar ce kai-tsaye bayan ya fito daga ziyarar da ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari a Aso Rock Villa, a ranar Alhamis.
Ziyarar dai da Tinubu ya kai wa Osinbajo ta ba-zata ce, domin mataimakin shugaban ƙasar bai san da zuwan na sa ba, sai dai ganin sa ya yi Are da tawagar sa tsulum a gidan sa.
Tinubu ya kai masa ziyarar ce bayan Osinbajo ya taya shi murnar cin zaɓe, tare da shan alwashin zai yi bakin ƙoƙarin sa wajen taya Tinubu kamfen domin nasarar lashe zaɓen 2023.
Majiya a gidan Osinbajo, wadda ba ta so a ambaci sunan ta, ta shaida wa wannan jarida cewa “ba zato ba tsammani sai ganin Tinubu aka yi a gidan, tare da Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu. Sai dai aka garzaya aka sanar wa Osinbajo cewa ga da Asiwaju ya shigo.”
Da ya ke jawabi, Tinubu ya ce ko kaɗan ba laifi ba ne don ya yi takara tare da Osinbajo. Ya ce dimokraɗiyya fa gaba ba ce.
Tinubu ya ce a zahirin gaskiya Osinbajo mutum ne nagari, mai amana, wanda sun daɗe tare.
“Osinbajo ya taimaka wa rayuwa ta, kuma ya yi tasiri a kafuwar siyasa ta. Ya taka rawa sosai a matsayin sa na babban lauya a shari’ar gwamnan jihar Osun da mu ka yi nasara.
“Kuma ba za taɓa mantawa ba yadda Osinbajo a matsayin sa na lauya, ya garzaya Landan ana maku-makun sanyi, amma sai da ya samo shaidar dangwala yatsa a can, wadda da ita ce mu ka yi nasara a zaɓen Osun.
“Don haka Osinbajo ya taimaka min a rayuwa ta, kuma ni da shi babu wata gaba ko ƙiyayya, mutu ka raba.”
Tinubu ya kayar da Osinbajo a zaɓen fidda gwani, inda ya samu ƙuri’u 1,271, Osinbajo ya zo na uku da ƙuri’u 235.
Discussion about this post