Shugaban ƙungiyar malaman jami’o’in ƙasar nan ASUU, Emmanuel Osodeke ya ce babu hannun ƙungiyar a asusun da Ahmed Isah ya buɗe wai jama’a su tara taro-sisi har naira biliyan 18 domin a baiwa ASUU don su janye yajin aikin da suke yi.
Idan ba a manta ba Ahmed Isa, mai gabatar da shirin Hembelembe a radiyon Human Right dake Abuja ya buɗe asusu inda yayi kira ga ƴan Najeriya su saka kuɗi domin tara naira biliyan 18 a biya malaman makaranta don su janye yajin aikin da suke yi.
Tuni dai har wasu da dama sun fara saka kuɗi a wannan asusu. Tuni har miliyoyi sun fara sauka cikin asusun.
Sai dai kuma shugaban ƙungiyar ASUU ya nisanta ƙungiya daga wannan asusu ya na cewa ba da yawun kungiyar ake tara kuɗaɗen ba.
Kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya sun ja daga watannin hudu kenan sasantawa bai yiwu ba a tsakani.
Daliban makarantun gwamnati kaf suna gida saboda yajin aikin.
Ra’ayoyin jama’a
Da yawa daga cikin mutane sun soki wannnan tara kuɗi da Ahmed Isah ya ƙirkiro, suna masu cewa wannan ba hurumi ne na sa ba.
” Niyyar da yake da shi yayi kyau amma kuma naira biliyan 18 ake magana. Idan aka ce ƴan Najeriya ne za su rika tara kuɗi suna baiwa malaman don su janye ya jin aiki ai koma baya kenan.
” Yau idan aka tara wannnan kuɗi aka baiwa malaman, gobe kuma idan hakan ya sake aukuwa yaya za ayi. Da abinci za a ji ko kuwa da tara wa malaman jami’o’i kudin albashi.
” Manyan Najeriya duk sun tura ƴaƴan su kasashen waje da makarantu masu zaman kansu a faɗin kasar nan. Dama dai ƴaƴan talakawa ne a jami’oin. Ta ina za a tara naira biliyan 18. Shi mai ba’a ya ke yi ko.
” Abinda ya fi da cewa shine ya ci gaba da amfani da kafar sa wajen yin kira ga gwamnati su gaggauta kawo karshen yajin aikin domin ɗalibai su koma makaranta. Hakan shine kawai gudunmawar da zai iya bada wa.
Discussion about this post