Kotun Shari’ar Haƙƙin Ma’aikata ta aza ranar 15 Ga Yuli domin yanke hukunci kan shari’ar da ake tafkawa ta neman a ƙara wa alkalan Najeriya albashi da alawus.
Mai Shari’a Osatohanmwen Obaseki ne ya aza ranar yanke hukuncin, bayan da lauyoyin ɓangarorin biyu kowane ya shaida wa kotu cewa ya gama gabatar da bayanai da hujjoji da shaidun sa.
Lauya Awomolo Adegboyega wanda ke wakiltar wanda ya shigar da ƙara, ya shaida wa kotu cewa masifar tsadar rayuwar da ake ciki a ƙasar nan ta sa tilas fa sai an duba albashin masu shari’a an yi masu ƙari.
Awomolo wanda babban lauya (SAN) ne, ya bijiro da matakai huɗu a kotu, kuma ya roƙi duk a biya masa buƙatar su.
Wani mai suna Sebastine Hon ne dai ya shigar da ƙarar.
Ya ce Hukumar Raba Kuɗaɗen Shiga Ga Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi (RMAFC) wadda ita ce ya kamata ta na ciki tsundun a cikin shari’a, ya ƙi gabatar wa kotun takardun bayanai ko ɗaya.
Wanda ya shigar da ƙarar dai ya maka Majalisar Dattawa da ta Tarayya ƙara ne, tare da Hukumar RMAFC kotu, sai Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami. Sai kuma Hukumar Kula da Ayyukan Shari’a ta Ƙasa (NJC)
Yayin da NJC ta goyi bayan shigar da ƙarar, Majalisa da Malami ba su yarda ba.
Babban Lauya Kunle Adegoke, wanda shi ne ya wakilci NJC, ya roƙi kotu ta amince da dukkan matakan ƙarin albashin wanda mai ƙara ya nemi a yi.
Adegoke ya ce rabon da a yi wa Alƙalan Najeriya ƙarin albashi, tun cikin 2008.
Ya nuna cewa ƙarancin albashin da masu shari’a ke fama da shi ya kassara rayuwar su sosai, kuma ya na ci gaba da ƙuntata wa rayuwar su, tare da kawo tawayar kasa biyan buƙatun ɗaukar nauyin iyalin da ya zama dole.
Ya ce babu adalci kwata-kwata a ce wai shekaru 14 cur ba a yi wa masu shari’a ƙarin albashi ba.
Majalisa ta soki batun ƙarin, bisa dalilin cewa wanda ya shigar da ƙarar ba shi da ‘yanci ko haƙƙin shigar da ƙarar.
Amma lauyan NJC ya ce shari’un da aka yi a baya sun nuna mai shigar da ƙarar na da haƙƙin maka su kotu, domin abu ne da ya shafi jama’a.
A kan haka ne ya ce ya zama dole a daina yi wa alƙalai sakayyar ba su lada ‘yar cikin cokali.
Awomolo ya ce magana fa ta ƙare, babu sauran wani kame-kame, tunda dai ɓangarorin biyu duk sun yarda cewa rabon da a yi wa alƙalai ƙarin albashi tun 2008.
A ƙarshe ya roƙi kotu ta tilasta wa Antoni Janar Malami ya daina cizon alƙalai, sai sun ji zafi wai sannan kuma zai nemi hura masu.
Amma lauyan Majalisa mai suna Charles Yoila bai yarda da Awomolo ba kwata-kwata.
Ya ma roƙi kotu ta cire sunan Majalisa a jerin waɗanda ake ƙara, domin ba a bi matakin da ya dace ba, wajen shigar da ƙarar.
Haka shi ma lauyan Abubakar Malami mai suna Ekene Elodimuo, ya rubuta wa kotu a rubuce cewa mai ƙarar ba shi da hurumin da zai maka su kotu.
A ranar 15 Ga Yuli ne dai za a yanke hukunci.
Discussion about this post