Ɗan takarar kujerar sanata na Kaduna ta Tsakiya Mohammed Abdullahi wanda aka fi sani da Dattijo ya antaya wa manoman Kaduna kyautar buhunan takin zamani domin noman bana da aka tsunduma gadan-gadan.
Manoman yankin Kaduna ta Tsakiya da suka kunshi mazaɓu 81 dake karkashin ƙananan hukumomin Giwa, Birnin Gwari, Chikun, Kajuru Kaduna Ta Arewa, Igabi da Kaduna Ta Kudu.
Ahmed Maiyaki wanda ya wakilci Dattijo a wurin taron ƙaddamar da raba takin ya ce wannan ƙyauta ce daga ɗan takaran domin manoman yankin da zai wakilta idan yayi nasara domin bunƙasa ayyukan gona musamman a wannan lokaci da damina ya fara kankama.
Ya roki waɗanda za su raba wa manoma taki su tabbata rabon takinbya kai ga manoman karkara.
” Ina kira a gareku, ku da zaku raba wa manoma wannan taki ku tabbata ya kai ga manoman karkara.
A karshe Dattijo ya yi kira ga sauran ƴan siyasa da su yi koyi da abinda ya yi domin taimaka wa manoma su sami kyakkyawan yabanya a daminan bana
Discussion about this post