Ƴan bindiga sun kai wa jerin gwanon motocin dake dauke da maniyyata aikin hajjin bana a jihar Sokoto.
An ɗauko maniyyatan daga karamar hukumar Isa za a kai su cikin garin Sokoto inda daga nan za su tashi zuwa kasar Saudiyya.
Wani mazaunin karamar hukumar Salihu Mustapha ya tabbatar da lamarin wa PREMIUMTIMES.
“Tun da gwamnati ta bude layin sadarwa daya sadarwa na wahala a jihar. Amma na samu labarin daga wani daga cikin matafiyan da maharan suka kai wa hari cewa maharan sun buda wa jerin gwanon wuta a dai-dai dajin Gundumi.
“Jami’an tsaron ‘yan sanda dake raka jerin gwanon maniyatan sun buɗe wa maharan wuta inda suka yi nasarar fatattakar su.
Kakakin gwamnan jihar Muhammad Bello shima ya tabbatar da haka yana mai cewa jami’an tsaron sun kuɓutar da matafiya babu wanda aka sace.
Shugaban hukumar jin daɗin alhazai na jihar Shehu Dange ya tabbatar da aukuwar lamarin sai dai bai yi karin haske game da harin ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sanusi Abubakar bai amsa wayarsa ba da sakonnin tes da aka aika wa wayan.
Jihar Sokoto na daga cikin jihohin Arewacin kasar nan da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.
Ƴan bindigan sun kashe mutane da dama, sun sace mutane, dabbobi da dukiyan mutane sannan da saka wa mutane harajin dole su na biya.
Discussion about this post