Akwai alamar cewa mutane sai fa sun koma garkame bakunan su da hanci da takunkumim fuska domin darkakowar cutar Korona a Najeriya yanzu.
Hukumar NCDC ta bayyana mutum 240 sun kamu da cutar daga ranar 8 zuwa 15 ga Yuni 2022.
NCDC ta ce mutum 63 sun kamu da cutar daga ranar Talata zuwa Laraba a jihohi biyu da Abuja.
Zuwa yanzu mutum 256,467 sun kamu sannan cutar ta yi ajalin mutum 3,144.
Mutum 3,123 na dauke da cutar Kuma mutum 250,154 sun warke a Najeriya.
Yaduwar cutar
NCDC ta ce bisa ga sakamakon gwajin da ta samu jihar Legas ne kan gaba wajen samu yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar nan.
A jihar mutum 50 ne suka kamu, Kano mutum 11 sannan mutum biyu a Abuja.
Sakamakon binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna cewa mututane sun rage kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar sannan da yin allurar rigakafin cutar a Najeriya.
Discussion about this post