Wata ƙungiyar matasan ƙabilar Ijaw da ke yankin Neja Delta, ta yi kira ga wakilan zaɓen ‘yan takarar PDP cewa a ranar fidda-gwani kada su yi gangancin zaɓen Gwamnan Jihar Ribas, Nysom Wike a matsayin ɗan takarar PDP na zaɓen shugaban ƙasa.
Ƙungiyar mai suna Ijaw Youth Council, ta ja hankalin waɗanda ta kira “yan uwan mu” waɗanda za su yi zaɓen fidda-gwanin takarar shugaban ƙasa na PDP cewa kada su zaɓi Wike ɗan yankin su.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a shafin ta na Facebook a ranar Talata, sun ce idan wakilan zaɓen ‘yan takara na yankin Neja Delta su ka zaɓi Nysom Wike, to sun ci amanar yankin su.
Kakakin IYC ne mai suna Ebilade Ekerefe ya sa wa sanarwar hannu, tare da rubuta tsinuwar ɓaro-ɓaro a kan duk wanda ya zaɓi Wike.
Idan ba a manta ba, Wike ya tsine wa ƙungiyoyin Matasan Ijaw (IYC) da Majalisar Al’ummar Ijaw (INC) a wani coci cikin Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas, a ranar Lahadi.
Gwamna Wike wanda ɗan takarar shugaban ƙasa ne a ƙarƙashin PDP, ya tsine wa mambobin ƙungiyoyin biyu ne saboda sun nemi gwamnatin tarayya ta saki Ɗan Majalisar Tarayya Farah Dagogo daga kurkuku.
Wike ne ya bayar da umarnin a kama shi, bayan ya yi ƙoƙarin hargitsa taron tantance ‘yan takarar gwamnan Jihar Ribas. Amma Dagogo ya ce ƙarya Wike ke yi masa.
Waɗannan ƙungiyoyi biyu dai sun bai wa Wike sa’o’i 48 ya tabbatar da an sako ɗan majalisar, wanda shi ma ɗan takarar gwamnan Ribas ne a ƙarƙashin PDP ɗin.
Wannan ne ya sa Wike ya tsine masu: “Allah ya sa rantsuwar aradu ta faɗo kan ku.”
Kakakin Ijaw ya ce abin da Wike ya yi masu zai iya kawo yankewar dangantaka tsakanin ƙabilar Ijaw da ƙabilar da Wike ya fito a cikin ta, wato Ikwere.
Sun yi wa Wike gorin cewa “ai dai Jonathan ne ɗan ƙabilar Ijaw ya tsayar da Wike gwamna, wanda ƙabilar Ijaw ɗin ba da son ran su ba.”
“Kenan tunda Wike ya yi addu’ar rantsuwar aradu ta faɗo kan Ijaw, ai har da Jonathan ya ke nufi kenan, mutumin da ya tsinto shi a rana, ya saka shi a inuwa.”
“Don haka mu na kiran duk wani ɗan ƙabilar Ijaw ya sani cewa Wike abokin gabar sa ne. Idan wakilan Ijaw su ka je wurin zaɓen fidda-gwani na ‘yan takarar shugaban ƙasa na PDP, kada su zaɓi Wike.”
Discussion about this post