A ranar Talata ce wasu mahara su ka bindige manoma 12 a gona, a ƙauyen Gakurɗi da ke mazaɓar Ɗaɗɗara, cikin Ƙaramar Hukumar Jibiya.
Majiya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES Hausa cewa bayan kisan manoman, maharan sun kuma ji wa mutum uku raunuka.
Wani mazaunin Ɗaɗɗara mai suna Bashir Salihu, ya shaida wa wakilin mu cewa manoman da aka bindige sun je gona ne domin aikin gyaran gonar shirin fara aikin daminar bana da ke gabatowa.
Ya kuma ce ‘yan bindigar sun banka wa wasu gidaje wuta.
Lamarin ya faru kwana biyu bayan da Gwamna Aminu Masari ya yi kakkausan ƙorafin cewa ‘yan bindiga sun lalata jihar, har Katsinawa sama da 13,000 sun yi hijira zuwa Jamhuriyar Nijar.
Jibiya inda aka kashe manoma 12 ta yi iyaka da Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar.
Kakakin ‘Yan Sandan Katsina Gambo Isa, ya tabbatar da afkuwar kisan.
Cikin bayanin sa, ya ce Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Katsina ya gaggauta zuwa Gakurɗi, inda aka yi jana’izar mamatan tare da shi.
Isa ya ƙara da cewa maharan sun dirar wa manoman ne a kan babura takwas, kuma su ka buɗe masu wuta.
Ya ce mutanen ƙauyen na da bindigogi, amma sai dai wani matashi ɗaya ne kaɗai ya tsaya aka yi artabu da shi da maharan.
An Yi Garkuwa Da Limaman Cocin Katolika A Katsina:
Kafin jijjifin asubahin ranar Laraba ɗin nan wasu ‘yan ta’adda su ka kutsa Cocin Katolika na Saint Patrick da ke ƙauyen Gidan Maikwano, su ka yi awon gaba da manyan limamai biyu da kuma wasu ƙananan yara biyu.
Gidan Maikwano na cikin Ƙaramar Hukumar Ƙafur.
Daraktan Hulɗa da Jama’a na Cocin Katolika ya shaida cewa lallai an yi garkuwa da mutanen, kuma su na barar addu’a.
Ya ce ‘yan bindiga sun tafi da babban limamin cocin ƙauyen mai suna Rabaran Stephen da mataimakin sa Oliver Okpara da kuma yara biyo ƙanana.
Wakilin mu ya kasa samun Kakakin ‘Yan Sandan Katsina domin jin ta bakin sa.