Ina mai matukar godiya ga Yan uwana, aminai na watau delegates na jamiyyar mu mai farin jini watau jamiyyar APC saboda kauna da jajircewa da kuka nuna mini shekaru da dama.
Kun zama a gareni wata haja wadda kimarta da muhimmancinta bashi misaltuwa a gareni. Saboda Amana da kulawa da kyautata wa da kuka nuna mini.
Jajircewa da kuka nuna shekarun baya da suka wuce ya tabbatar min da cewa son ci gaban Adamawa da dorewarta sune makasudin taimakon da kuke nuna min don mu tsamo jihar Adamawa daga Koma bayar da take ciki.
Ina son in tabbatar muku da cewar zanci gaba da aiki kafada da kafada daku don cinma babban burin mu Wanda shine ganin Samar da mafita ga jihar Adamawa da mutanenta.
Kuma Ina son in shaida muku cewar, bazan taba daukar kyautatawa, gudummawa da taimakon da kuke bani da wasa ba Kuma bazan ci amanar ku ba ko in manta da irin kwazon ku don mu cimma burin mu na Samar da sabuwar jihar Adamawa.
Ina mai jaddada muku cewar har abada bazan manta da taimako da kauna da kuke nuna min ba Kuma INSHA ALLAHU ba zan baku kunya ba.
Ina mai jaddada muku cewar zanci gaba da hada Kai daku domin Samar da jihar Adamawa wadda kowa zai yi alfahari da ita musamman yayanmu da jikokin mu.
Ina Kara shaida muku idan muka ci gaba da hada karfi da Karfe, za mu Kai ga gaci a wannan muhimmiyar tafiya tamu.
Amma wannan tafiyar tana da matukar wahala saboda kalubale kala kala da ake samu. Amma Allah zai Kai mu ga Nasara idan muka ci gaba da jajircewa. Kuma Ina muku alkawarin cewa wata rana INSHA ALLAHU zamu kaiga gaci.
Daga karshe Ina Kara jaddada biyayya ta ga jamiyyar mu mai farin jini akan ci gaba da yin aiki tukuru don jaddada Martabarta da Kuma nasararta.
Ina mai godiya a gareku gaba daya.
Nine naku
Mal. Nuhu Ribadu